Kishin Kasa: Idan babu kasa babu rayuwa (3)

Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, matukar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jarraba yaki da juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an […]

Kishin Kasa: Idan babu kasa babu rayuwa (3)

Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, matukar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jarraba yaki da juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an yi asarar rayuka da dukiya mai yawa. A kan dole aka dawo aka zauna a matsayin kasa daya. Ke nan, babu abin da ya dace da mu illa mu fitar da bangaranci daga zukatanmu, mu fuskanci kasa gaba daya, ta yadda za mu samu ci gaban da ya dace da mu.

Wata mummunar dabi’a da ke yi wa kishin kasa karan-tsaye kuma take janyo wa kasa koma baya, ita ce dabi’ar nuna wariyar addini. Babu shakka wannan dabi’a tana taka rawa wajen haddasa hairani da rashin hadin kai a Najeriya. Lallai ne ’yan kasa su tashi tsaye wajen cijewa da daurewa wajen zama da juna tare da daraja addinan juna, ba tare da nuna yatsa ga wadanda ba addinanmu daya da su ba.

Kamar yadda za mu lura, Allah cikin ikonSa da hikimarSa, Ya halitta kuma Ya kadarta mutane masu mabambantan akida da addini su rayu a cikin kasa daya. Idan kowane mai addini ya cije wuri guda ya ce dole sai ra’ayin addinisa za a bi domin a tafi tare, lallai kam haka faufau ba za ta yiwu ba. Idan haka ne, kuma haka din ne ma, to ina dabara, ina mafita? Akwai ta, kuma guda daya ce. Abin yi shi ne, a matsayinmu na ’yan kasa daya, kowa ya rike martabar addininsa, ya bi darussan da ke shimfide cikin addininsa sau-da-kafa, ba tare da ya kawo wa dan uwansa mabiyin wani addini cikas ba. Idan aka yi haka, shi ke nan, an huta da ka-ce-na-ce. Kai mabiyin addinin Kirista, sai ka ci gaba da bin Kiristancinka, kai ma mabiyin Musulunci, sai ka ci gaba da bin Musuluncinka. Hatta ma wadanda ke bin addinin gargajiya, tunda dai su ma ’yan kasa ne, sai su ci gaba da bin nasu addinin. Shi ke nan, husuma ta kare, babu hairani.

A matsayinka na Musulmi, idan kana son mutane su shiga addininka, sai ka bi hanyar da Allah Ya huwace maka, ta nuna kyakkyawan misali, wato ka rika mu’amala mai kyau da nuna halayya tagari ga al’umma, kamar yadda addininka ya koya maka. Za ka rika yin rayuwa ta tawali’u, kana aiwatar da komai cikin gaskiya, adalci da amana da son al’umma. Wadannan kyawawan halaye, za su zama abin koyi kuma abin sha’awa ga sauran al’umma. Ta haka sai ka ga wadanda ba mabiya addininka ba suna sha’awarka, suna sha’awar rayuwarka. Babu mamaki idan ka yi musu tayi, su shigo su ma su zama Musulmi.

Haka shi ma mabiyin Kiristanci, idan har yana son wani ya shiga addininsa, abin da zai yi ke nan. Wato ya bibiyi rayuwarsa cikin aminci da gaskiya da adalci. Idan aka yi haka, shi ke nan an huta da husuma.

Wani abin da ya kamata mu fahimta shi ne, duk wani addini, matukar na kirki ne, to manufarsa ita ce samar da tsira da ci gaban dan Adam. Babu wani addini da ya amsa sunansa da ya amince da ka uzura wa wani ko ka yi wa wani ta’addanci. Duk wani addini na mutunci, burinsa shi ne ya jagoranci dan Adam zuwa ga aikata kyawawan ayyuka kuma ya hana shi aikata munana. Don haka, kishin kasa ne ga dan kasa ya jure wa zaman tare tsakaninsa da abokin zamansa, koda kuwa addininsu ya bambanta.

Yana kuma daga kishin kasa ga mutum ya kasance mai tafiyar da al’amuransa cikin gaskiya da amana, wato ya guje wa ha’inci. A yayin da rikon amana da gaskiya suka kasance jigogin kishin kasa, shi kuwa ha’inci ya kasance makamin ruguza kasa. Sai mu kama dabi’un kirki, mu watsar da na banza, matukar dai muna son mu ga muna samun ci gaba da bunkasa.

Yaudara, halayya ce mai saukin aikatawa, amma illar da ke tattare da ita tana da yawa. Ba kishin kasa ba ne ga dan kasa ya kasance cikin halayyar yaudara, domin kuwa babu abin da take haifarwa sai koma-baya ga al’umma da kasa baki daya. Ke nan, ya zama wajibi mu guji yaudara, tun da dai na tabbata babu mai son ya ga cewa wani ya yaudare shi. To, dan uwa, abin da ka san cewa ba ka son a yi maka, yaushe kuma kai za ka yi wa wani? Babu hikima cikin wannan ko kadan.

Wadannan dabi’u: Shashanci, tambele, hassada, gaba, gilli da ayarinsu, dabi’u ne da tuni suka kauce wa hanyar kwarai kuma duk wanda ya siffatu da aikata su, bai kasance dan kishin kasa ba. Lallai ne mu kaurace musu, domin mu kasance ’yan kasa nagari masu kishin kasa da kishin al’umma.

Wajibi ne a gare mu mu kasance masu bin dokokin kasa, kamar yadda aka shimfida su. Ta hanyar bin dokokin ne za mu samu tafiyar da al’amuranmu cikin tsari da inganci. Idan kuwa muka kasance muna zama cikin karya doka, muka zauna zaman-kara-zube, babu babba babu yaro, to rayuwarmu ba za ta sha bamban da ta dabbobi ba. Idan haka ta faru, shi ke nan mutuwar kasa ta zo, wanda kuma ba haka aka so ba, wai kanen miji ya fi miji kyau.

A yayin da muke rufe wannan maudu’i, zan yi kira ga al’umma, manyanmu da kanananmu, mazanmu da matanmu cewa lallai ne mu tashi tsaye mu ceto kasarmu, mu kasance masu kishinta na kwarai, masu sonta da kishin ci gabanta. Kada mu bari ta fadi ko ta ruguje, domin kuwa ba mu da wata kasa kamarta.

Wassalam. Sai kuma mun hadu a mako na gaba.