Kishin kasa ne mafita ga ’yan Nijeriya – Sarkin Hausawan Kwatano

Jagoran Hausawan a Kwatano ya kuma roki Gwamnatin Nijeriya ta tausaya wa talakawa.

Kishin kasa ne mafita ga ’yan Nijeriya – Sarkin Hausawan Kwatano

Taswirar Nijeriya

Kungiyar ’Yan Nijeriya Mazauna Jumhuriyar Benin ta ce, “matsalolin daban-daban da Nijeriya ta samu kanta a ciki suna iya ci gaba da aukuwa muddin aka kasa yin maganin matsalar cin hanci da rashawa.

Shugaban Kungiyar kuma Sarkin Hausawan Kwatano Alhaji (Dakta) Mouhamadou Muniru Garba Nakura ne ya bayyana haka yayin hira da Aminiya a Ibadan.

Sarkin ya kuma ce, idan mahukunta suka rufe ido wajen daukar matakin ba-sani-ba-sabo ga dukkan masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta hanyar satar kudin gwamnati, to kuwa ’yan Nijeriya musamman talakawa za su mike kafa su ci moriyar arzikin kasar haihuwarsu.

“Duk da yake kasar Benin ta kasance kamar wani yanki ne a cikin Nijeriya da ta dogara da ita ta fannonin tattalin arziki, sai dai matsalolin hauhawar tashin farashin kayan abinci da kayan bukatun yau da kullum da ya haifar da tsadar rayuwa ga ’yan Nijeriya a yanzu babu irin su a kasar Benin.

“An samu hakan ne a dalilin daukar matakin daidaita farashin kayan masarufi da mahukunta a kasar Benin suka yi, wanda ana iya shafe shekara 20 masu zuwa a nan gaba ba tare da farashin kaya ya tashi ba.”

Jagoran Hausawan a Kwatano ya kuma roki Gwamnatin Nijeriya ta tausaya wa talakawan da suka zabe tare da yin adalci, musamman ta fannin daukaka darajar Naira da karya darajar Dala da bayar da wadatattun kudin Dala da Sefa da Yuro ga ’yan kasuwa masu odar kaya daga Turai.

Daukar irin wannan mataki tabbas zai kawo saukin matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasarmu.

Sannan ya yi kira ga ’yan Nijeriya Musulmi da Kirista da masu Addinin gargajiya da marasa addinin a ko’ina suke zaune a duniya su sanya kishin kasar haihuwarsu a gaba.

Sarki ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su jingine bambancin addini da kabilanci da bangaranci waje daya, wanda hakan shi ne zai kai kasar ga rike ragamar jagorancin Afrika baki daya kamar yadda kasar China ta yi a duniya.

Alhaji Muniru Garba Nakura ya zo garin Ibadan ne ziyarar domin ta’aziyar rasuwar dan uwansa da ya rasu a kwanakin baya.