Kishin matasa da mata ya sa na fito takarar Gwamnan Kaduna –Hajiya Fatima
Hajiya Fatima Muhammad ita ce ’yar takarar Gwamnar Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyar Restoration Party ( RP), a zantawa da ta Aminiya ta bayyana abubuwan da za ta mayar da hankali a kai idan aka zabe ta Gwamnar Jihar: Me ya jawo hankalinki kika shiga takarar Gwamnan Jihar Kaduna? Da farko dai babu abin […]
Hajiya Fatima Muhammad ita ce ’yar takarar Gwamnar Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyar Restoration Party ( RP), a zantawa da ta Aminiya ta bayyana abubuwan da za ta mayar da hankali a kai idan aka zabe ta Gwamnar Jihar:
Me ya jawo hankalinki kika shiga takarar Gwamnan Jihar Kaduna?
Da farko dai babu abin da ya janyo hankalina na fara neman takara a matsayina na mace sai saboda kishin in taimaka wa matasa, saboda yadda nake ganinsu suna zama babu aikin yi. Ina kuma so idan na samu dama in bunkasa sana’o’i ta yadda matasa da mata za su samu aikin yi, musamman bangaren noma; dole mu inganta shi domin jama’armu su samu abin yi ta hanyar samar musu kayayyakin aiki na zamani domin rage masu wahalar noma. Idan Allah Ya ba mu mulki, za mu samar da fili babba a matsayinmu na gwamnati inda matasa za su rika yin aiki da za su samu amfani mai kyau har su rika taimaka wa na kasa da su. Burina in ga mata da matasa na cikin walwala domin su ne kashin bayan ci gaban kasa.
Ga shi kina takara a jam’iyyar da ba kuwa ya santa ba, kuma akwai manyan jam’iyyu ciki har da wadda Gwamnan Jihar ke takara a cikinta, ko kina ganin akwai nasara a tafiyar?
Insha Allahu muna ganin za mu samu nasara saboda matasa da mata mu suka saka a gaba kuma su ne akasarin masu kada kuri’a a kasar nan. Su ne ma siyasar baki dayanta kuma su suka bukaci mu fito mu nemi wannan kujera wanda hakan ya sa muke tunanin samun nasara in Allah Ya yarda.
Mata na fuskantar kalubale sosai a siyasar kasar nan ta wacce hanya za ki kauce wa haka?
Gaskiya akwai kalubale masu yawa amma dole ne mu kauce musu idan har muna so a yi da mu a kasar nan. Daya daga cikin hanyoyin da za mu magance wadannan kalubale shi ne mu shigo mu nemi mukaman nan. Idan Allah Ya sa muka kafa gwamnati za mu samar da hanyoyin tallafa wa mata da sauran ’yan kasa.
Ko jam’iyarku na da ’yan takara a sauran jihohi?
Eh, akwai su a jihohi kamar Kano da Osun da sauransu kuma dukansu mata ne masu neman kujerar Gwamna.
Ke nan jam’iyar mata ta fi bai wa fifiko?
A’a, ta dai bai wa mata goyon baya ne kawai domin idan ka lura duk sauran jam’iyun maza suke bai wa fifiko amma sai wannan jam’iyyar tamu ta ga ya dace ta bai wa mata dama domin su fito su nuna bajintarsu wajen neman kujerun Gwamna. Sun karkafa mana gwiwa ne domin mu fito mu nuna ko in ce mu ba da tamu gudunmawar wajen ciyar da kasar da al’ummarmu gaba.
Ba ki ganin tsayar da mace da Gwamna El-Rufa’i ya yi a matsayin mataimakiyarsa na iya iya dakile damarki ta zama Gwamna?
Ko kadan. Ya ma kara min kwarin gwiwa ne saboda hakan ya nuna cewa mata na da muhimmanci. Gaskiya wannan karin karfin gwiwa ya yi min domin in kara jajircewa don ganin na samu goyon bayan jama’ar jihar nan a zabe mai zuwa.
Wadansu na ganin cewa manyan jam’iyyu na dakile kananan jam’iyyu a kasar nan me za ki ce?
Gaskiya hakan na faruwa sosai amma za mu yi iya kokarinmu wajen ganin mun tabuka abin a-zo a-gani a zabe mai zuwa. Muna sa ran samun kujerar da izinin Allah domin komai nufi ne na Allah. Don haka muna rokon Allah Ya ida mana nufinmu.
Kina ganin za ki iya kayar da Gwamna mai ci?
(Dariya) Eh, to abu ne na zabe, idan Allah Ya ba mu nasara shi ke nan, idan kuma Allah bai ba mu nasara ba, sai mu goya wa wanda ya ci baya.
Idan Gwamna mai ci ya nemi ki janye daga takara ki goya masa baya za ki yi?
Wannan wani abu ne kuma na daban, amma idan muka tabbatar zai aiwatar da kudirorin jam’iyyarmu na taimaka wa mata da matasa da samar da tsaro ga al’ummar jihar kila. Kuma ka san sha’anin mulki ba na mutum daya ba ne, don haka ba za mu janye ba kai-tsaye sai dai a hada gwamnatin hadin gwiwa kuma ko shi din ya danganta da abin da jam’iyarmu ta amince da shi domin mu dai mun fito ne da zuciya daya domin taimaka wa mutanenmu.