Kishin Qasa: Muhimmancinsa da tasirinsa ga rayuwar al’umma (1)
Tare da sallamar da muka saba, ya ku masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i ne, wanda zai yi mana tambihi game da kishin qasa da kuma muhimmancinsa ga al’umma. Kamar yadda al’amura suka gudana, a kwanakin bayan ne muka gudanar da bukukuwan cikar […]
Tare da sallamar da muka saba, ya ku masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i ne, wanda zai yi mana tambihi game da kishin qasa da kuma muhimmancinsa ga al’umma.
Kamar yadda al’amura suka gudana, a kwanakin bayan ne muka gudanar da bukukuwan cikar Najeriya shekara 57 da samun mulkin kai. Dangane da haka, a matsayinmu na ’yan qasa, ya dace mu gane muhimmanci da tasirin kishin qasa da kuma dangantakar da ke tsakanin qasar tamu da kuma mu kanmu.
Abu na farko da ya kamata kowane dan qasa ya gane shi ne, qasarka ita ce alqiblar rayuwarka. Abin nufi a nan shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin qasar nan kake. Ya Allah kana cikin qauye ne ko a birni, kai dan qasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a qarqashin qaramar hukuma, a qarqashin jiharku; wadanda su kuma suke a cikin Najeriya.
Kasancewar ba ka da wata qasa da ta kai qasarku, lallai ne ka maida hankali wajen nuna kishinta da kare martabarta, domin kuwa idan ta kasance mai muhibba da martaba, to kai ne ka zama mai martaba da muhibba. Idan kuma ta zama ballagaza, marar kima a idanun duniya, to ka sani kai ma haka kake.
Domin ganin ka zama mutum nagari, mai kima da martaba, sai ka tashi tsaye, ka yi qoqari iya yin ka, wajen bunqasa qasarka. Dalili na farko ke nan da ya sanya za ka zama mai kishin qasa. Amma idan zan qara yin wata tambayar kuma, ta yaya za ka zama mai kishin qasa? Ta yaya kishin qasarka zai amfane ka, ya amfani al’ummar qasarka da kuma ita kanta qasar?
Yana daga cikin kishin qasa, ka kasance mai gaskiya da amana a cikin al’amuranka. Idan ka kasance mai fadar gaskiya kuma kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan kuma ka kasance mai riqon amana wajen mu’amalarka da mutane, to kuwa qasarka za ta zama mai gaskiya da amana, abar qauna ga al’ummar duniya. Dalili shi ne, a matsayinka na dan qasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da amana. Idan kai ka zama haka, wancan shi ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; shi ke nan an samu abin da ake so. Qasarmu za ta cika da masu gaskiya da amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintatta kuma mai aminci a cikin qawayenta na sassan duniya.
Kishin qasa ne ga dan qasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wanda ba ya aiki ko sana’ar komai. Da zarar dan qasa ya zauna durshan ba tare da yana wata harka ba, babu wanda zai zame masa aboki sai Shaidan. Wannan zaman banza zai bijiro masa da tunane-tunane marasa kyau, sannan su ingiza shi zuwa aikata munanan ayyuka, wadanda za su kasance halaka a gare shi kuma wadanda za su cutar da sauran al’umma. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi qasarsa, domin kuwa sunanta zai baci ta hanyar munanan ayyukansa.
Don haka, ya dace mutum ya miqe tsaye ya sama wa kansa abin yi. Kada mutum ya ce zai zauna sai ya samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Koda ka gama jami’a ne, idan ba ka samu aiki ba, yi qoqari ka fara koda aikin qarfi ne na qwadago. dan abin da za ka samu, zai iya zama mai albarka kuma ka biya buqatarka da shi. Kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunquri da ka yi na aikin qarfi, Allah na iya hada ka da wata sila, wacce za ka iya samun aikin da ya fi shi.
Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci koda da qaramin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya. Sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka riqa samu, madamar kana adanawa da kadan-kadan; jarinka yana iya zama mai girma. Idan dai har ka riqa gudanar da harkarka cikin gaskiya da tsare haqqin jama’a, kasuwancin naka yana iya zama mai albarka. Domin kuwa, akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da qanqanen jari kuma suka bunqasa har suka zama hamshaqan ’yan kasuwa.
Ala-ayyi-halin dai, zaman kashe wando, ko zaman jiran mai yawan da ko alamarsa babu, alhali babu tabbas, ba abin dogaro ba ne. Don haka, kishin qasa ne ga mutum ya hana kansa zaman kashe wando, ya cire girman kai daga zuciyarsa, ya yunqura domin neman na halal komai qanqantarsa.
Kishin qasa ne ga mutum ya kasance mai qaunar jama’a, ba tare da nuna wariyar qabilanci, bangaranci ko addinanci ba. Kada ka ce za ka yi mu’amala ne kawai da ’yan qabilarka ko kuma ka ce ’yan qabilarka ne kadai mutanen kirki, don haka babu ruwanka da wasu. Idan ka yi haka, babu shakka ba ka nema wa qasarka alheri ba kuma ba ka zama mai kishinta ba. A lokacin da ka dauki ’yan qabilarka kawai a matsayin mutane, ka banzatar da sauran jama’a, kawai domin su ba naka ba ne, to lallai akwai matsala. Na farko dai, kai kanka za ka gamu da matsala, domin kuwa al’ummar qasarka sun kasance qabilu daban-daban, masu yaruka daban-daban, masu al’adu daban-daban, kuma ya zama wajibi su yi rayuwa tare da wasu qabilun, tunda duk ’yan Najeriya ne. Wata rana, dole ne za ka nemi wata buqata, wacce dan qabilarka ba zai biya maka ita ba. Idan haka ta kasance, to yaya za ka yi, tun da ba ka dauke su a bakin komai ba?
Za mu ci gaba