Kishin Qasa: Muhimmancinsa da tasirinsa ga rayuwar al’umma (2)
Gare ku masu bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’in a makon jiya, yau kuma za mu ci gaba daga inda muka tsaya; wato inda muke yin bayani game da illar da ke tattare da kabilanci. Idan mun duba da idon basira, duk wani addinin da ya […]
Gare ku masu bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, kamar yadda muka faro wannan sabon maudu’in a makon jiya, yau kuma za mu ci gaba daga inda muka tsaya; wato inda muke yin bayani game da illar da ke tattare da kabilanci.
Idan mun duba da idon basira, duk wani addinin da ya amsa sunansa, ba ya son al’umma su nuna wariyar kabilanci. Babban burin kowane addinin kwarai shi ne, al’umma su kasance tsintsiya daya, ta yadda za su amfani juna wajen zamantakewa da mu’amala. Hasali ma, Allah (SAW) Ya shaida mana cewa Ya halicci al’umma ne zuwa kabilu da jinsuna daban-daban, ba don komai ba sai domin su fahimci junansu. Wannan yana nuna mana cewa, maimakon mu rika nuna kyama da wariya ga kabilun da ba namu ba, kamata ya yi mu fahimci juna, ta yadda za mu amfani juna kuma mu ci gajiyar juna.
Wannan ne ma ya sanya na tuno da wani kalami da wani jigon al’umma, mai kishin kasa da al’ummarsa ya taba furtawa. Ina maganar Gamji dan kwarai ne, wato marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello. Kamar yadda aka ruwaito, an ce marigayi Dokta Nnamdi Azikiwe ne ya taba ce masa su mance da bambance-bambancensu… Shi kuwa Gamji sai ya ce masa ba haka za su yi ba, madamar suna son fahimtar juna.
Kamar yadda aka ruwaito, Sardauna ya ce wa Zik su zo su gane bambance-bambancensu sai su fahimci juna, su yi aiki tare alhali suna masu kiyaye hakkokin juna. Ya ce Zik Inyamuri ne, shi kuwa Bahaushe. Zik mutumin Kudu ne, shi kuwa dan Arewa. Zik Kirista ne, shi kuwa Musulmi. Ta haka za su hada hannu su yi wa kasa hidima.
Kuma wannan al’amari, ta kowane janibi muka duba shi, za mu gane tasirinsa, kasancewar kowa na bukatar kowa. A yayin da Allah Ya hore wa wannan kabila wannan baiwa, Ya kuma hore wa waccan wata baiwar ta daban. Sai a hadu tare, kowa ya baza kolin tasa baiwar domin amfanin juna. Wannan shi ne kishin kasa kuma da na al’umma.
Idan muka dauki mummunan halin nan na bangaranci kuwa, shi ma muninsa daya da kabilanci. Madamar muna son mu kasance ’yan kishin kasa, masu son ganin al’umma ta samu ci gaba, dole ne mu rungumi juna, ba tare da la’akari da bangaren da junanmu suka fito ba. Babban abin da a har kullum ya kamata mu rika kallo shi ne, kasa daya ke gare mu, wacce ita ce mallakinmu. Ba mu da wata kasa da za mu iya kira tamu face ita. Ke nan da zarar Kudu ta bunkasa, to Najeriya ce ta bunkasa, haka ma Arewa.
Kamar yadda kowace kabila ke bukatar wata kabila, haka ma bangarorin kasar nan ke bukatar juna. A yau idan muka duba, za mu ga yadda ’yan bangarori daban-daban suka bar yankunansu, suka tafi wani yanki daban, suna rayuwa. A Legas ko Ibadan ko Ekiti, za ka ga Hausawa da Fulani suna gudanar da rayuwarsu, kamar yadda a Katsina da Kano Da Sakkwato za ka ga Yarabawa suna gudanar da nasu al’amuran.
A Borno da Bauchi da Yobe, za ka ga Inyamurai suna sha’aninsu na yau da kullum, kamar yadda za ka ga sauran kabilun Arewa a Fatakwal da Benin da sauran yankunan Kudu. Wanna ya nuna cewa lallai kasa daya muke, kuma duk muna bukatar juna. Ke nan sai mu taru mu aiwatar da abin da ya dace, wanda zai ciyar da kasar gaba, ba tare da wariyar bangaranci ba.
Haka kuma, Allah Ya yi wata hikima, inda Ya warwatsa rahamarSa a dukkan sassan kasar nan, ta yadda ya zama wajibi mu yi zaman tare a matsayinmu na ’yan kasa daya, madamar dai muna son cin gajiyar arzikin juna. A yayin da Allah Ya zuba dukiyar abinci da nama da fadin kasa falala a yankin Arewa, sai kuma Ya malala arzikin makamashin mai da iskar gas a Kudancin kasar nan. A lokacin da ’yan Kudanci ke bukatar abinci da nama da sauran kininsu, mu kuma nan bangaren muna bukatar makamashi. Dalili ke nan ma ya zama wajibi mu hada hannu, mu nuna kishin kasa da kishin juna wajen cudanya da juna cikin fa’ida; ta yadda za mu bunkasa kasarmu. Wannan shi ne kishin kasa.
Babu yadda za mu ce mu samu ci gaba, madamar muna kyarar juna, muna yakar juna. Idan har za mu waiwayi tarihi, ai iyayenmu sun taba jaraba yakin juna, inda aka fafata Yakin Basasa. Babu wani bangare da ya ci ribar wannan yaki, alhali kasar gaba daya ta yi asara. A wannan yaki, an yi asarar rayuka da dukiya mai yawa. Akan dole kuma aka dawo aka zauna a matsayin kasa daya. Ke nan, babu abin da ya dace da mu illa mu fitar da bangaranci daga zukatanmu, mu fuskanci kasa gaba daya, ta yadda za mu samu ci gaban da ya dace da mu.
Za mu ci gaba