Kisisinar kishiya
Kisisina da sanabe da feleke da daukacin nau’ukan iya yi, su aka san kishiya da su, amma ba karya kafar jariri ba. Kodayake an santa da kissa, sai dai ba ta kisa. Haurobiyawa mun sha ta shi da ban ta’ajibin yadda kishiya ke yi wa jarirai kisan mummuke, ta hanyar kassara rayuwar su. Kuma duk […]
Kisisina da sanabe da feleke da daukacin nau’ukan iya yi, su aka san kishiya da su, amma ba karya kafar jariri ba. Kodayake an santa da kissa, sai dai ba ta kisa. Haurobiyawa mun sha ta shi da ban ta’ajibin yadda kishiya ke yi wa jarirai kisan mummuke, ta hanyar kassara rayuwar su. Kuma duk wanda ya bibiyi shafukan amintattun jaridun kasar Haurobiya, tun daga watan Yawon-wuni zuwa makon farko na Yawon-wulli ya sha ganin ko karanta labaran yadda kishiya ta karya kafar jinjiri, har ma da wadda ta yanke wa dan mijinta al’aura.
A da irin wadannan batutuwa ba su cika bijirowa ba, sai dai karon-battar kishiya da kishiya, inda aka sha ruwaito yadda wata ke korar wata daga gida, ta hanyar kisisina ko kulle-kulle tsatsuba da tsubbace-tsubbace. Wata kuwa ba ta bin boka bare malam, amma saboda iya sanabe da kantakarya da gwalangwaso sai kawai maigida ya ji cewa, wadda ba ta iya feleken ba, ba ta burge shi ko ma ta fita daga zuciyarsa kwata-kwata. Kuma a mafi yawan lokuta a kan samu cewa, an mayar da kishiya da kishiya sun zama ’ya’yan bora da mowa. Sanin kowane matar da ake yi wa lakabin ‘Ladan na-duke,’ ita aka fi yi wa cin kashin kaji. Ita kuwa idan ba mai natsuwa ba ce, maimakon ta yi na-damo har Mai-duka ya kawo mata mafita sai ta biye wa kishiya da maigida a yi ta cakusawa, har a karke da katse igiyar turken aurenta.
Da zarar an kai ga datse igiyar turakun ma’aurata, sai a yasar da ’yan dugwi-dugwi su yi ta walagigi tsakanin wannan gidan dangi da wancan, domin sun shiga kangi, cikin su ya yi ta kugi, tamkar ana kada musu gangi. A irin wannan yanayi ake fifita ’ya’yan mowa a kan na bora. Daga nan kuma an dauki hanyar tarwatsa iyali, ko haifar da gaba da giba har a zo ana cewa, a raba, a raba.
Batu na ingarman kwangiri ba don kada a ce na zuga iyayen giji ba, ai da na dauko zuga-zugi, na yi ta hura musu wuta kan lallai su yi kissa da kisisina, amma ban da kisa. Mata a yi sanabe, amma ban da sababin sabatta ’yan dugwi-dugwi; a yi feleke keke da keke, amma ban da kisan mummuke; a tsube tsaba tsibi-tsibi, amma ban da tsubbace-tsubbace. Idan kuwa kun ki ji, to tabbas bokaye da ’yan bori na iya jefa ku cikin taskun bautar Tsumburburar Tsatsunburun, har ta kai ga an samu wadanda za su tsumbure, wato dai ’yan tsibbu sun yi furfure da su.
Kai iyayen giji, alo tsiya, alo danja, kai ban da tsikarin uwar miji da tabarya.’ Duk da cewa wannan batu karairaye-karairayen maganganun yaren Hau-hau ne wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa, amma matukar aka tsikari Iya da tabarya, ko nuni da muciya, ai sai in ce an yi tabargaza da baranbarama. Kuma idan aka ci gaba da haka za a tsikaro tsiya da wasali kasa, shi ke nan tsi ta ja ya!
Lallai a samu uwa tagari da za ta tarairayi ’yan dugwi-dugwi, a hada kan iyalai, don samun zuri’a tagari, wadda za ta fitar da ’ya’yan Baba da Inna daga cikin rukukin kangin rayuwa. Yin hakan ya zama dole, domin kowane tsuntsu kukan gidan su yake yi,’ kun ga ke nan ta haka za a samar da jagororin al’umma nagargaru, masu aiki tukuru don kawar da duk wani jimamin jamhurun jamhuriyar kasar Haurobiya. Kuma a daina yawon-dara wajen wassafa wa al’umma cewa, a tsarin dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson-siya-siya su yi ta yin jinkiri da jimirin cin jinbiri.
Kai kuwa ja-gaban iyali ina mai jan na-zomonka, kan lallai ka da ka kuskura ka sawo wa waccan ‘AZABURI-KARYA, alhali wannan ka danka mata ‘HOLLANDAISE da SUPERWAd’ ko nau’ukan atamfofi da shadda da siliki da leshi na alfarma. Irin wannan rashin adalci da ake yi wa mata, shi ke haifar da yamutsin iyali, musamman idan an fifita MOWA a kan BORA.
Ba don malam Bahaushe ya kakaba wa kurun sa tagiyar Malam Mantau ba, ai sai in ce shi ya jawo mana wannan matsalar karya kafa da tsinke gaban jariri, domin tun muna ’yan dugwi-dugwi ake yi mana tatsuniyar JANNIYA-JANNATI.
A cikin tatsuniyar Janniya-jannati, akwai wakar da ake yi wa dan kishiya, ko dan dugwi-dugwi, wanda mahaifiyarsa ba ta gidan mahaifin sa, inda za ku ji kakarku ta takarkare tana cewa:
Janniya jannati
Kishiyar uwa ba uwa ba ce
Janniya jannati
Za ta ba ka tuwo da magani
’Yan makaranta ku samu wata tsohuwar ta karasa muku tatsuniyar nan, don ku ji inda aka ce Janniya jannati ya rika binne abincin da kishiyar uwa ta ba shi ko a turken ingarma ne? Oho ni dai na kakaba wa kurunguna tagiyar Malam Mantau. Shi ya sa na kasa kara tatsuniyar Janniya Jannati.
Ni dai nasan cewa, kishiyar uwa, uwa ce, da kuma na kowane. Don haka zan iya tuna cewa lokacin da Hajiya Kanusiyya, matar Gizo-gizon-dakin-gwaggo za ta turke ’yarta a turken rayuwa, ai daukacin kishiyoyinta sai da suka zo, suka tayata murna. Hasalima wannan umarni ne daga Maigidan su Malam na bayan kango. Kowa ya kama, aka yi kama-kama har aka samu aka turke wannan yarinya a turakar mijinta.
Kuma nasan iyayen giji, wadanda suka tarairayi ’ya’yan kishiyoyi, har ta kai ga a yau su ke cin gajiyar tarairayar ’yan dugwi-dugwi da suka yi, shi ya sa ma ake yi musu biyayya. Saboda haka ina mai bayar da shawara a duk sa’adda mutum ya daura niyyar zuwa kARAYE, to ya tsaya tsaf sai ya famfare a birnin FARAYE, sannan ya himmatu ka’in da na’in wajen faranta ran ’ya’ya da iyaye. Sai ka ji idan an ce AHAYYE, IYE! Wasu kuwa sai su amsa da IYE NANAYE. Domin ta haka ne kawai za a samu dan nagoye, nagoye, har ma da ’yan yaye ko tagwaye; gajeru da dogaye; mazaje da mataye. A daina duk wasu jaye-jaye.
‘Idan ana biki, wata ba ta daura zanen wata.’
‘Taka nazumbude, taka nazumbude!
‘Ban da aron zane, ban da aron zane!’
Haurobiyawa, a daina bugun taiki an kyale jaki. Lallai a yi kokarin kwakulo musababbin karon battar kishiya da kishiya. Kai hatta FANCAL-FANCAL din FACALA ba abin yasar wa ba ne, tunda irin wannan tsilli-tsillin matsaloli su ne tushen illata rayuwar ’yan dugwi-dugwi. Alhaki dai an ce kwikuyo ne, kuma laifi tudu ne, saboda haka mu daina take namu muna hango na kishiya. Ka da mu rika kashe maciji ba mu sare kan sa ba. A yi duk abin da ya dace wajen kawar da JUHALA don tabbatar da ADALA dangane da zamantakewar iyali.