kissar matar da ta je wajen malami don ta mallake mijinta

Assalmu Alaikum. Yau ma kamar kowane lokaci ina dauke da wannan maudu’i wanda ya zama wajibi a gare mu mu fadakar da mata akan hakkokan dake kansu na mazajen su wanda tsare su shi ne babbar hanya ta mallakar miji ba tare da boka ko malam ba. A kowane lokaci na fusknaci mata a kan […]

kissar matar da ta je wajen malami don ta mallake mijinta
kissar matar da ta je wajen malami don ta mallake mijinta

Assalmu Alaikum. Yau ma kamar kowane lokaci ina dauke da wannan maudu’i wanda ya zama wajibi a gare mu mu fadakar da mata akan hakkokan dake kansu na mazajen su wanda tsare su shi ne babbar hanya ta mallakar miji ba tare da boka ko malam ba.

A kowane lokaci na fusknaci mata a kan wannan gaba nakan fada masu cewa “kyautatawa gami da tsarewa mazaje hakkokansu su ne babbar hanyar mallake miji”.
Wata mata ce ta je wajen wani malami (mai tsoron Allah) ta ce masa “Allah Ya gafarta malam so nake ka yi mini aiki domin in mallake miji na”.
Sai malamin ya girgiza kai da ya nuna akwai jan aikin dake da akwai. Ya ce mata zai mata aiki amma sai da sharadin in za ta kawo masa nonon barewa wanda ta tatso shi da hannun ta”.
Da yake an ce sa kai ya fi bauta ciwo, sai matar ta yi shiri ta hada kayanta ta nufi dokar daji kuma ta yi sa’a ta iske wata barewa ta yi sabuwar haihuwa, sai kuwa ta samu wata itaciya ta haye sama ita kuma barewar da ‘ya’yanta suna kasa.
Sai ya kasance duk lokacin da barewar nan ta tafi neman abinci sai matar nan ta sauka ta dauke ‘ya’yan nan daya bayan daya ta a je su gefe guda ta share masu wurin da ta dauke su sannan ta mayar da su wurinsu na asali.
Duk lokacin da uwar ta dawo sai ta iske an share wajen sai ta yi mamaki, har ta kai matar nan tana jinkirta sharar nan har barewar ta dawo ta iske ta tana wannan aiki, haka za ta sa mata ido sai ta gama ta maida su inda suke.
Yau da gobe har ta kai matar nan tana shafa ‘ya’yan barewar nan in suna shan nono har tana iya cire wani daga jikin nonon ta sanya wani.
In gajarce maku labari saboda kyautatawa har matar nan ta zama tana sarrafa barewar nan duk yadda ta ga dama. A karshe ta dauko dan gorarta ta kara jikin nonon barewar nan ta tatsa ta cika ba tare da ata matsala ba sannan ta tattara kayanta sai gida.
Bayan ta koma gida sai ta shirya ta nufi wajen malamin nan rikk da gorar nonon sannan ta mika masa. Koda ya amsa sai mamaki ya kama shi ya tambayeta ya aka yi har ta samu nasarar samun nonon?
Matar nan ta share wuri ta fada masa duk hanyoyin da ta bi har ta samu ta cimma burin ta. Sai malamin nan ya gyara zama ya ce ta saurare shi da kyau da kuma kunnen basira. Yaci gaba da cewa “har ga Allah duk abinda zai mata ba zai tasiri ba matukar ba ta bi mijinta sau da kafa wajen kyautata masa kamar yadda ta yi wa wannan barewa ba”.
Sai mamaki ya kamata ta ce “ka fa san maza yadda suke da wuyar sha’ani”, sai malamin ya ce “ta je ya ba ta nan da wata guda idan har ta aikata kwatankwacin abinda ta yiw a barewar nan ba ta samu kan mijinta ba to ta dawo shi kuma zai yi mata aikin da za ta mallake shi har abada”.
Suka yi ban kwana ta yi masa godiya ta koma gida. Bayan tsawon wata guda sai ta koma wajen malamin nan rungume da jaka makare da kayan arziki ta mika masa kuma ta nuna farin cikinta ganin mafarkinta a yau ya zama gaskiya.
Daga karshe Malam ya ce mata “wannan shi ne asirin da har abada ba zai kare ba sai ma karin tagomashi na yardar Allah da za ki samu “. Domin Annabi (SAW) ya ce “duk matar da ta mutu alhali mijinta yana mai yarda da ita to za ta shiga aljanna”.
Da wannan nake kira ga matanmu da su ji tsoron Allah, wallahi zuwa wajen boka kafirci ne kuma duk wadda ta mutu a wannan tafarki wuta ce makomar ta. Allah Ya tsare mana imaninmu, Allahumma Ameen.
Sanusi Hashim Abban Sultana. Daga Jihar Katsina 08065507271.