Ɓangaren Lafiya Na Cikin Mummunan Yanayi A Gwamnatin Tinubu — Likitoci
Gwamnatin Tinubu ta haifar da cikas ga al’amuran kiwon lafiyar al’umma a ƙasar nan.
Ƙungiyar Ma’aikatan Kiwon Lafiyar Jama’a ta Najeriya (APHPN), ta koka kan yadda bangaren ke cikin haɗari a karkashin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Alphonsus Isara, Shugaban APHPN ne ya bayyana haka a ranar Talata a wajen taron shekara-shekara karo na 40 da ke gudana a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Taken taron na bana shi ne “Bude Sabon Shafi Domin Inganta Matsayin Ɓangaren Kiwon Lafiyar Jama’a.”
- Abin Da Addini Yace Game Da Azumin Ƙananan Yara
- Babu gawar mutumin da aka tsinta a gefen hanya a Kano — ’Yan sanda
Isara ya bayyana cewa, gwamnatin Tinubu ta haifar da cikas ga al’amuran kiwon lafiyar al’umma da ke barazana ga tsarin kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce, akwai kalubale daban-daban da suka haɗa da karancin ma’aikatan lafiya da ya samo asali daga yawan tafiyar da ƙwararru a fagen kiwon lafiya ke yi zuwa ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, wanda aka yi wa sara da JAPA.
Haka kuma, ya bayyana rashin wadatattun kayan aiki a matsayin wani babban al’amari da ke shafar ɓangaren kiwon lafiya a Najeriya.
Hakazalika, ya bayyana cewa “Kalubalen tattalin arziki da yanayin zamantakewar al’umma a halin yanzu yana kawo cikas ga ɓangaren kiwon lafiya.
Ya kuma bayyana rashin kayan aikin likitanci da suka haɗa da magunguna daga cikin manyan matsalolin da ke ciwa harkokin lafiya tuwo a ƙwarya a Najeriya.
Shugaban APHPN ɗin ya kuma bayyana cewa dole ne a gaggauta magance matsalolin da ake fuskanta domin gujewa faɗawa hatsari.
Isara, ya bayyana cewa mambobin kungiyar ta APHPN suna ba da shawara a taron da ke gudana tare da gabatar da kasidu don samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu a fannin kiwon lafiya a kasar.
Ya ƙara da cewa, ƙungiyar na son haɗa kai da ma’aikatar lafiya ta tarayya da hukumomin kiwon lafiya a ƙasar nan domin bullo da shirye-shiryen da za su inganta harkokin kiwon lafiya a Najeriya.
Ya ce, ’yan Najeriya na fuskantar bullar cututtuka da dama irinsu Zazzabin Lassa, Zazzabin Tifot, Kwalara, da kuma Sanƙarau, yana mai jaddada cewa ƙungiyar za ta ba da shawarar yin amfani da ka’idojin rigakafin kamuwa da cutuka a cikin al’umma da kuma matakan ci gaba a Najeriya.
Isara ya yi kira da a kafa ma’aikatar kula da lafiyar jama’a a dukkan cibiyoyin kiwon lafiya a makarantun sakandare da manyan makarantu a Najeriya.