Kiyaye ran dan Adam shi ke sa a samu zaman lafiya a kasa

Wani malamin addinin musulunci Sheikh Abubakar Salihu Dengi, ya ce ’Kiyaye ran dan adam shi ne yake sa a samu zaman lafiya a bayan kasa. Kuma zama lafiya shi ne yafi komai muhimmanci a bayan kasa saboda babu abun da za a iya aiwatarwa matukar babu zama lafiya. Hatta abinci ba za a iya ci […]

Kiyaye ran dan Adam shi ke sa a samu zaman lafiya a kasa

Wani malamin addinin musulunci Sheikh Abubakar Salihu Dengi, ya ce ’Kiyaye ran dan adam shi ne yake sa a samu zaman lafiya a bayan kasa. Kuma zama lafiya shi ne yafi komai muhimmanci a bayan kasa saboda babu abun da za a iya aiwatarwa matukar babu zama lafiya. Hatta abinci ba za a iya ci ba idan ba zama lafiya‘. Shaihin malamin wanda Hedkwatar Kungiyar JIBWIS ta kasa a Abuja ta tura shi Jihar Oyo domin yin wa’azin watan Ramadan na bana ya fadi hakan ne cikin ganawarsa da wakilinmu jim kadan bayan kaddamar da rabon tallafin kudi na Naira miliyan daya da dubu 170 da suturu ga marayu da gajiyayyu da zaurawa da reshen Bodija na kungiyar JIBWIS ya yi a ranar Lahadi da ta gabata.

Sheikh Abubakar Dengi wanda a cikin wa’azinsa ga al’ummar musulmi a manyan masallatan Kungiyar JIBWIS na Sabo da Bodija da Ojo da Sasa da Akinyele a Jihar Oyo ya mayar da hankali ne a kan matsalar tabarbarewar tsaro a Najeriya ya ce, ‘Allah (SWT) Ya bayar da muhimmanci ga girmama ran dan adam, shi ne yasa ya kafa doka mai tsanani ga dukkan wanda ya yi aikin da zai kai ga salwantar ran dan adam. Da yake amsa wata tambaya Shaihin malamin cewa, ya yi ‘Alhaki ne da aka dora a kan kowane dan adam ba tare da la’akari da matsayin mutum ba domin kowa yana da rawar da zai taka wajen tabbatar da tsaron kasa. Akwai abubuwan da suka rataya a wuyan bangaren gwamnati akwai kuma abubuwan da daidaikun jama’a za su yi musamman wajen yawaita addu’o’in rokon Allah da bayar da bayanan abubuwan da za su iya zama barazanar tsaro ne ga mahukumta domin zaman lafiya da kwanciyar hankali.’ Shugaban Kungiyar JIBWIS a Jihar Oyo Alhaji Salisu Abdullahi da Shugaban reshen kungiyar na Bodija Alhaji Sani Ibrahim Dandare Jega su ne suka jagoranci manyan baki wajen mika tallafin kudi da suturu ga marayu 203 da gajiyayyu 70 da zawarawa. Babban Limamin masallacin JIBWIS na Bodija Ustaz Marwanu Musa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Gidauniyar marayu da gajiyayyu da zaurawa ya yi kiran ga al’ummar musulmi masu abun hannu su rinka yin amfani da dukiyarsu wajen tallafawa rayuwar irin wadannan mutane. Alhaji Sani Ibrahim Dandare Shugaban reshen kungiyar na Bodija ya nuna farin cikinsa da kasancewar reshensa ne yazo na daya a bana wajen tara kudade da suturu duk da cewa abun da aka samu a bara ya dara na bana.