kiyayyar da ake wa Musulunci da Musulmi

Kafin zuwan Musulunci, duniya ta kasance a cikin yake -yake da zubar da jinane. Ana zaluntar mata ta hanyar bautar da su da tauye su, ba su da ’yanci, ana hallaka su. Masu karancin samu ko talakawa an ajiye su a matsayin da bai gaza na dabbobin daji ba. Mai karfi ne kadai ke da […]

kiyayyar da ake wa Musulunci da Musulmi
kiyayyar da ake wa Musulunci da Musulmi

Kafin zuwan Musulunci, duniya ta kasance a cikin yake -yake da zubar da jinane. Ana zaluntar mata ta hanyar bautar da su da tauye su, ba su da ’yanci, ana hallaka su. Masu karancin samu ko talakawa an ajiye su a matsayin da bai gaza na dabbobin daji ba. Mai karfi ne kadai ke da gaskiya. Bautar gumaka da dodanni da kuma addinan gargajiya ne ke baje kolinsu. Duniya tana tsananin bukatar mai taimako da zai fitar da ita daga cikin wannan tsananin duhun jahilci da bata. dan Adam yana bukatar mai ceto da zai kawo karshen wadannan bala’o’i da musgunawa.
Haske ya keto, ya kore duhun da duniya ke ciki ta hanyar aiko da Manzon tsira da sako na karshe a matsayin cikamakin Annabawa, kuma shugaban Manzanni Annabi Muhammadu (SAW). Ya zo da addinin Musulunci, wato mika wuya ga Allah Mahalicci, zuwa ga dukkan duniya. Domin fitar da mutane daga duhun kafirci da zalunci  da almundahana da jahilci da tabarbarewar tarbiyya da suka dabaibaye duniya. Kamar yadda Allah (SWT) Yake cewa “A yau Na kammala muku addininku Na cika ni’imaTa a gare ku, Na yardar muku da Musulunci a matsayin addini.” A karkashin inuwar Musulunci an tanadar wa kowane mai hakki, hakkinsa. Mutum ya samu hakkinsa, dabbobi ma sun samu nasu hakkin. Musulunci ya shar’anta shari’o’i saboda a kiyaye hakkoki a tsarkake kowa da kowa.
Amma a yau, kafiran duniya sun yi dirar mikiya a kan Musulunci da Musulmi. Mun wayi gari a matsayin bayi mun zama marayu a garuruwanmu da gidajenmu, ba mu da ta cewa ba mu isa mu sa ko mu hana ba. Duk mai sanye da rigar Musulunci ana masa kallon dan ta’adda.
A yau Musulmin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka (CAR), sun tsinci kansu a cikin mawuyacin hali, ta’addanci da cin zarafi da keta alfarmar dan Adam ke wakana a kansu. Duk mai amsa sunan “Musulmi” yana cikin kangin rayuwa da bakin zalunci da rashin ’yanci da walwala. Rashin imani da kuma rashin tausayi da ke faruwa a can ya wuce duk tunanin mai tunani! Kisan kai na kare dangi da kona gidaje da gawarwakin jama’a da fyaden da ake yi wa matansu da wasoson dukiyar Musulmi abin sai dai a yi shiru kurum. Dubban Musulmi sun yi kaura sun fantsama sun bar gidajensu da dukiyoyinsu da iyalansu. A makonni kadan da suka wuce, an samu wani dan ta’adda Kirista, wanda ya fi dabba dabbanci da ya rada wa kansa suna, “Mahaukacin Kare,” ya kashe wani Musulmi ta hanyar sassara shi, kuma ya dauki naman jikinsa yana ci danye a bainar jama’a, tare da nuna alfahari da gadara.
Wannan da me ya yi kama? Kai ko dabba ba na jin za ta iya cin naman dabba ’yar uwarta da suke jinsi daya. Har ila yau dai rikicin ya rutsa da wani tsohon minista da ya rasa ransa ta hanyar kisan gilla! Laifinsa yana amsa sunan “Musulmi.” Ina Majalisar dinkin Duniya? Ina kasashen Yammacin Duniya suke? Da kuma kungiyoyin rajin kare hakkin bil Adama? Idan har ’yan luwadi da madigo an ce suna da ’yancin rayuwar da suke so, su fa wadannan bayin Allah da jinanansu ke kwaranya, kamar ambaliyar ruwa daga teku, rayukansu kullum salwata suke ba su da ’yanci ne? Hatta sojojin Faransa da ke kasar a halin yanzu ana zarginsu da nuna halin ko-in- kula game da abin da ake yi wa Musulmi. Dama haka ake kare ’yancin dan Adam din?
Ya bayyana a zahiri cewa, babu wani kwakwaran mataki da kasashen duniya ke dauka domin kawo karshen wannan balahirar, shin shi Musulmi ba ya da ’yancin rayuwa a kasarsa ta haihuwa ne? Saboda ikirarin da matasan Kirista ke yi na cewa sai sun karar da duk wani Musulmi a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Michel Djotodia, Musulmin farko da ya fara mulkin kasar, ya nuna kyakkyawan misali ta hanyar sauka daga mukaminsa, domin samun zaman lafiya. Amma hakan bai kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa ba. Wannan na nuna cewa an tasam ma kawar da Musulmi ne daga kasar baki daya. Ina manyan kasashen Musulmi na duniya suke? Irin su Saudiyya da Iran da katar da Indonesia da Malaysia da Masar da Pakistan da sauransu? Ina malaman addinin Musulunci? Ina Hizbulllahi da Hamas? Duk sun yi shiru ana ta zubar da jini bayin Allah dare da rana! Dama haka ake Musuluncin? Wannan ita ce ’yan uwantakar addinin? Shin mun tanadi amsar da za mu ba Allah a gobe kiyama, in ya tambaye mu game da sauran ’yan uwanmu Musulmi? Saboda haka lokaci ya yi ya ku al’ummar Musulmi! Da za mu koma ga addininmu, mu rike shi da karfi.
Ya zama wajibi mu hada kai, domin fuskantar kalubalen da ke tunkararmu. Kada mu yarda jam’iyyu ko kungiyanci da kabilanci ko darikanci ko bangaranci ya ci gaba da ruguza mu. kasashenmu dole ne mu rika yin abu daya, kare Musulunci da Musulmi, musamman hakkin bauta ga kowa hatta wadanda ba Musulmi ba. Ya wajaba a kanmu rika nuna so ga addininmu da nuna fushinmu kan taba shi. Mu yanke hulda ko dangantaka da duk wadanda suke cin zarafinsa. Mu daina yin duk wata mu’amala da su, mu daina sayo komai daga gare su.
Daga karshe mu sani fa Musulmi Allah Ya kira mu a cikin Alkur’ani, kuma shi ne sunan da Ya ba mu. Mu jefar da son zuciya mu hada kai a kan gaskiya. Ya ku ’yan uwana a Musulunci! Lallai abin da zai dawo mana da martabarmu shi ne komawa ga addini da hadin kai da kuma addu’a. Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kaskantar da kafirci da kafirai. ’Yan uwanmu Musulmi da ake kashewa kullum a sassan duniya ya Ubangiji! Ka karbe su a matsayin shahidai, Ka kuma tsare mu daga dukkan sharrin makiya da kaidinsu, amin.
Injiniya Jibril Abdul Daura
08038997861
Daura Construction Company,
Daura, Jihar Katsina.