Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus
Nagelsmann mai shekara 38 ya sabunta kwantiraginsa ne a watan Janairun 2025, wanda zai ƙare a shekarar 2028.
Rahotanni daga Jamus sun ce ana shirin raba gari da kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, Julian Nagelsmann, bayan ficewar da ta yi tun a zagayen ’yan 32 na Gasar Kofin Duniya.
Jaridar Bild ta ruwaito cewa an tattauna da Nagelsmann na tsawon sa’o’i uku a hedikwatar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jamus (DFB) da ke Frankfurt, inda aka ce an gabatar masa da tayin euro miliyan bakwai a matsayin diyya domin ya ajiye aikinsa.
Nagelsmann mai shekara 38 ya sabunta kwantiraginsa ne a watan Janairun 2025, wanda zai ƙare a shekarar 2028.
Ficewar Jamus bayan shan kashi a bugun fenariti a hannun Paraguay ta jawo suka, kasancewar ita ce karo na uku a jere da ƙasar ke gaza wuce matakin farko na wasannin fitar da gwani a Gasar Kofin Duniya, bayan ficewarta tun daga matakin rukuni a gasannin Rasha da Qatar.
Shugaban hukumar ta DFB, Bernd Neuendorf, ya sanar a ranar Talata cewa an fara lalubo matsaloli da dalilan da suka sa Jamus ta gaza a gasar.
Rahotanni sun ce ana sa ran yanke hukunci kan makomar Nagelsmann nan da farkon mako mai zuwa.
Kafofin yaɗa labarai da dama na Jamus, ciki har da Sky Germany da Süddeutsche Zeitung, sun bayyana cewa tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, shi ne kan gaba wajen maye gurbin Nagelsmann.
Klopp ya daina aikin horaswa bayan barinsa Liverpool a shekarar 2024, kuma a halin yanzu yana aiki a matsayin shugaban harkokin ƙwallon ƙafa na kamfanin Red Bull, inda yake kula da cibiyar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da kamfanin ke tallafawa a ƙasashe daban-daban.