Ko aikin hajjin bana zai yiwu kuwa?
Aikin Hajji shi ne na biyar a jerin shika-shikan Musulunci biyar. Sauran su ne Fadin Kalmati shahada da kudurce da yin aiki da abin da ta kunsa, wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu SAW bawanSa ne kuma manzonSa ne na karshe. Sai tsayar da Sallah, sai bayar da Zakkah da […]
Aikin Hajji shi ne na biyar a jerin shika-shikan Musulunci biyar. Sauran su ne Fadin Kalmati shahada da kudurce da yin aiki da abin da ta kunsa, wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu SAW bawanSa ne kuma manzonSa ne na karshe. Sai tsayar da Sallah, sai bayar da Zakkah da kuma azumtar azumin watan Ramadan. Dukkan wadannan ayyuka guda biyar suna bukatar kudurtawa, sannan aikatawa walau da gabbai ko da dukiya, kamar bayar da Zakka da aikin Hajji kansa, wasu ma suna bukatar samun cikakkiyar lafiya, kari a aikin Hajji ma har da ta hanya, kafin aiwatarwa, kamar yin Sallah da zuwa Aikin Hajjin, wato dai ma`ana wasu sai da lafiya da wadata, wasu kuma ba sa bukatar kudi, muddin dai kana raye, to, akwai bukatar ka aiwatar da su.
To kuwa tunda Aikin Hajji ne ya kasance sai ka niki gari ka bar garinku da kasarku, ka tafi kasa mai tsarki wato kasar Saudiyya, ko a can din ma akwai wasu kebantattun garuruwa da wurare da Allah SWT Ya shardanta a yi Aikin na Hajji, kafin ya zama karbabbu gare Shi, to, kenan babu mamaki a ce daga lokaci zuwa lokaci kasar ta Saudiyya tana sa sababbin ka`idoji da sharudda wani lokaci ma har da dokoki don tafiyar da babban aikin ibadar.
A irin wannan tafiya ce yanzu ake da bayanan wasu sababbin sharudda da ka iya kiransu masu tsauri da kasar ta Saudiyya ta bullo da su ga Maniyatan aikin Hajjin na bana wadanda har aljihonsu, sai sun taba. Alal misali zuwa yanzu a karon farko kasar ta Saudiyya ta bullo da haraji akan kayayyakin da aka ri ga aka sarrafa da wanda duk zai sayi kaya ko a yi masa wata hidima sai ya biyasu, harajin da ake ma lakabi BAT. A bisa ga wannan sabon haraji da kasar ta Saudiyya ta dora shi akan sutturu da wutar lantarki da sadarwa da aka azama haraji kashi 5 cikin 100. Man fetur ma kasar ta Saudiyya ta yi karin farinsa, kasancewar man fetur sha kuru-kundum ne a cikin tafiyar da tattalin arzikin kasa, tuni rahotanni ke tabbatar da cewa harkokin sufuri da kayayyakin marmari da gayyaki (da akasari dama shigo da su ake kasar), farashinsu ya daga, hatta kofin shayi farashinsa an ce ya tashi, kar ka yi batun su lemon kwalba ko na kwali da makamantansu.
An ruwaito daya daga cikin Mahukuntan kasar ta Saudiyya Yari Muhammad bin Salman, yana cewa ta wadannan kare-kare, kasar ta Saudiyya za ta samu karin kudaden shiga da su ka kai Dalar Amurka $21biliyan, duk shekara, yana mai kafa hanzari da cewa karin ya wanzu ne a dalilin faduwar farashin man fetur ya yi warwas. A gefe daya kuma an ce mahukuntar kasar su na ta kokarin ganin irin matakan da za su dauka wajen saukaka wa `yan kasa tsadar rayuwar da suka fada. Mai karatu, ka iya cewa dai wannan zance ne, don kuwa babu wata kasa da ta taba karin haraji ko farashi a kan man fetur da wutar lantarki (dukkansu manya-manyan makamashi ne) da fannin sadarwarta, sannan kuma ta ce tsadar rayuwa ba za ta samu jama`arta ba.
Bayan batun haraji akwai kuma sabon tsarin da kasar ta Saudiyya ta fara amfani da shi, wanda shi ma zai kara kawo mata kudaden shiga, wannan shiri shine na dukkan Maniyacin da ya je Aikin Hajji ko Umrah cikin shekaru uku da su ka gabata, to, kuwa in ya tashi komawa sai ya biya kasar ta Saudiyya harajin yi masa takarda iznin shiga cikin kasar wato bisa, har kudin kasar SR 2,000, wadannan kudade koda a canjin gwamnati Maniyaci zai same su na N305 akan kwace Dalar Amurka daya, to sai ya biya N162, 666.66k, kar ka ce kuma ga abin da wanda zai je Aikin Hajji ko Umrah ta jirgin yawo da ko da Bankinsa ya tunkara sai ya sayi Dalar a kan N365 zuwa N366 koma fi. Kasancewar a Aikin Hajjin bara 2017, shi ne mafi tsada da `yan kasar nan su ka taba gani, wanda ya kai Ni.5miliyan, a zaman kujera mafi karancin guzuri, kasancewar a barar gwamnati ta bayar da canjin kowace Dala akan N305, sabanin a bara waccan da ta ba da ga canjin akan N197. A bana ba a sa ni ba, ko akan canjin N305 din za ta ba Maniyatan ko kuma a farashin canjin Bankunan kasuwanci na N365, za ta ba Maniyatan. Idan akan na Bankunan kasuwancin ne kuwa, to, mai karatu na barka da lissafi a kan yadda Hajjin banan za ta kasance.
Bayan batun kudaden zuwa Aikin ibadar da irin tsadar rayuwar da Maniyata za su taras a kasar mai tsarki, batun da har yanzu Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa bata fito ta ce uffan ba akan yadda kudaden tafiyar za su kasance, duk kuwa da tuni ta sanar da Hukumomin jihohin jin dadin Alhazai na jihohi da babban birnin tarayya, yawan kujerun da ta basu a aikin Hajjin na bana, ta kuma nemesu da lalle su kawo wani kaso na Maniyansu don kama masaukai da sauran ayyukan ibadar nan da 16 ga watan Maris mai kamawa. A bana dai kasar ta Saudiyya ta kebewa kasar nan jimlar Maniyata 95,000, da su ka hada da Maniyatan jirgin yawo 10,000.
Wani babban batu da na ji karamar Ministar Harkokin kasashen waje Hajiya Hadizah Abba Ibrahin na ji tana kokawa da shi, lokacin da ta bayyana gaban Kwamitin Aikin Hajji na Majalisar Wakilai ta tarayya, har ta nemi taimakon `yan Majalisar akan yadda za a shawo kan al`amarin tun lokacin aikin Hajjin bai kure ba, shi ne na sabon tsarin daukar cikakken bayanin kowane Maniyaci a kan na`ura mai aiki da kwakwalwa, kafin ma ta ba shi iznin shiga kasarta don aikin Hajjin banan. Ba wai samar da bayanan ba ne babbar matsala, babbar matsalar kamar yadda Ministar ta ce bai wuce Cibiyoyi uku rak a Legas da Abuja da Kano da Mahukuntar kasar ta Saudiyya suka ce nan Kamfanonin da ta amince su yi aikin. Mai karatu Hajiya Hadiza da masu Kamfanonin harkokin yawan bude idanu da suke aikin kai Maniyata, tuni suka koka da neman mafita a kan yadda za a shawo kan wannan matsala da yanzu suke fama da ita, bisa ga irin kwanakin da ake yi kafin na`urar ta kammala bayanan Maniyaci.
Saura da me, kowa ya san yadda yanzu duniya ta zama cikin rikici, musamman na `yan tada kayar baya, masu kai hare-hare da muggan makamai su kuma yi mummunar barnar da ke haddasa asarar daruwan rayukan al`umma da dukiyoyinsu a cikin wani dan karamin lokaci. Ba zai zama wani abin mamaki ba, idan kasar ta dauki matakan kandagarki, musamman a lokacin taron al`ummar musulmi da ba irinta a duk duniya, amma kuma lalle akwai bukatar kasar ta Saudiyya ta kara yawan Cibiyoyin da za su yi wannan daukar bayanai, ta yadda a kalla kowace jiha a ce tana da Cibyoyi daga 20, zuwa abin da ya samu gwargwadon yawan Maniyatanta. Ba zan iya kaddara irin rudani da kuncin da za a jefa Maniyatan bana ba akan wannan sabon shiri. Mai karatu ka kaddara ko da Maniyatan jihohi shiyyar Arewa maso Yamma za a ce a tantance a Kano, kawowarsu da komawarsu lami lafiya kadai ya isa abin dubawa a wannan lokaci. Ko ba a son Musulmi su je aikin ibadar.