Ko akwai abin koyi a shugabancin Jihar Zamfara?
A wannan makon, MALAM NASIR JA’AFAR (08036532789), [email protected] mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya aiko mana nazarinsa game da yadda al’amuran shugabanci suka canja a jiharsa ta Zamfara, daga mulkin cima-zaune zuwa aikin raya kasa da bunkasa al’umma. Ga abin da yake cewa:Tun farkon halittar bil’adama, mutum ya kasance yana amfani da hanyoyin […]
A wannan makon, MALAM NASIR JA’AFAR (08036532789), [email protected] mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya aiko mana nazarinsa game da yadda al’amuran shugabanci suka canja a jiharsa ta Zamfara, daga mulkin cima-zaune zuwa aikin raya kasa da bunkasa al’umma. Ga abin da yake cewa:
Tun farkon halittar bil’adama, mutum ya kasance yana amfani da hanyoyin sadarwa ne domin neman abinci, muhalli, tsaro da kuma ilimi ta hanyar gurgusawa daga wannan wuri zuwa wancan. Bayan tsawon lokaci ne sai ci gaban duniya ya samar da wasu sabbin hanyoyin ta hanyar sauyawar hanyoyi da kuma sauyin ababen hawan. Hanyoyin zirga-zirga na farko sun fara a kafa, ruwa da kuma dabbobi; amma ci gaban zamani da ilimin kimiyya ya haifar da samuwar hanyoyi mafiya sauri da sauki a fannin zirga-zirga na duniyar yau.
Babbar manufar fadada hanyoyin tituna shi ne kusanto da al’umma tare da habaka tattalin arzikinta. Muhimmancin wannan bangare a kan bunkasa tattalin arzikin jama’a da walwalarta ya kai mizanin da babu abin da za a iya kwatanta shi da shi a dukkan ma’auni. A dayan hannu kuma za mu tarar cewa babban dalilin da ke haddasa ci bayan al’ummu ba ya rasa nasaba da rashin ingantattun hanyoyin zirga-zirga na tituna da sauran hanyoyin sufuri a tsakanin mutane.
Idan muka yi tsinkaya zuwa ga kasashen da suka ci gaba, za mu tarar cewa habakar tattalin arziki, walwalar jama’a da ayyukan yi ga jama’a ya samu nasara ne a dalilin sanya jari mai gwabi a bangaren hanyoyin sufuri. Ba shakka, sanya jari a wannan sashe shi ne jigo kuma tubalin gina kyakkyawan shugabanci da bunkasar tattalin arzikin kowace al’umma mai fadi-tashin samun ci gaba. A kasar Bangaladesh, jigon nasararsu wajen magance talauci shi ne saukakawa da inganta hanyoyin zirga zirgar kayayyakin masarufi da wadanda aka sarrafa a tsakanin birane da kauyuka ta hanyar shimfida ingantattun hanyoyin tituna. Wani misalin kuma shi ne Amurka, wacce a tsakanin 1980 zuwa 1991 ake alakanta kashi daya bisa biyar na bunkasar tattalin arzikinta a kan sanya jari mai yawa a sashen ayyukan gina tituna, wanda ya hada da manya-manyan hanyoyi da kuma na cikin garuruwa.
Wani abun lura a nan shi ne, lallai nagartattun hanyoyi da sauran ababen da ke taimakawa tsarin sufuri bai tsaya ga zamowarsa kashin bayan habaka tattalin arziki ba ta hanyar sufurin mutane da hajoji a cikin sauki, arha da aminci ba kawai, amma hakan yana kuma share fagen samar da ayyuka ga miliyoyin jama’a har ya zama su na samar da kaso mai amfani ga kansu da kasa baki daya ta hanyar dogaro da kai da rage yaduwar munanan ayyukan assha wanda zaman-ci-ma-kwance ke iya haifarwa. A kan haka za mu iya cewa, lallai harkokin sufuri da zirga-zirga za su iya samar da akalla kaso goma cikin dari (10%) na jimillar hajojin cikin gida a duk shekara; musamman a yanayin tabarbarewar harkokin hada-hada na wannan lokaci.
Bugu da kari, samar da kyakkyawan yanayin sufuri yana da matukar tasiri a rayuwarmu ta yau da kullum a dukkan fuskoki. Idan aka kyautata, aka kuma inganta tsarin gudanarwar hanyoyin sufuri, kamar shimfida kyawawan tituna, to hakan na fassara mana samuwar kyakkyawan yanayin safara a cikin sauri da biyan bukata a kan kari, saukaka shan mai ga ababen hawa da kuma rage gurbacewar muhalli; ga kuma rage salwantar rayuka. A karshe dai sai a tarar babu bata lokaci da yawa ko kuma kuncin tafiya a tare da al’ummomin da za su ci gajiyar wadannan ayyuka na romon dimokuradiyya, musamman ’ya’yan Jihar Zamfara da ma ’yan Najeriya baki daya. Hakazalika, kyakkyawan tsarin tituna yana taimaka wa rage cunkoson hanyoyi wanda hakan ke saukaka lamurran tsaro ga kasashen da suka ci gaba, kai har ma da masu tasowa, wadanda ke amfani da hanyoyin zamani a titunansu wajen samar da tsaro da irin na’urorin zamani. ’Yan sanda da ma’aikatan lafiya za su iya kawo dauki a cikin sauki kuma a kan kari, a duk inda aka sami hatsari, wanda hakan ba karamin amfani yake da shi ba ga majinyata ko mabukacin agaji a cikin gaggawa.
Ga duk wata gwamnati da ta san ciwon kanta, take kuma kishin ci gaban al’ummarta, ya zama wajibi ta yi koyi da irin salon jagorancin Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar da takwaransa na Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa irin hobasar da suka yi na mayar da hankali kacokan wajen fadada ayyukan tituna da nufin magance matsalolin da ake fuskanta kan sha’anin sufuri a wannan kasa, tare da kawar da shingayen da suka shamakance harkokin tattalin arzikinmu a wannan yanki na Arewa-maso-yamma, da zimmar samar da sabbin hanyoyi na farfadowar harkokin kasuwanci a kasa baki daya.
Babu shakka, Gwamnan Zamfara, Dokta Abdul’aziz Yari ya nuna bajinta wajen ganin jiharsa ta shiga a sahun gaba na rukunin ’yan ajin farko na kasashen duniya a karni na 21. Gwamnatinsa tana da kyakkyawan tsari tare da dukufa wajen aiki tukuru domin kai wa ga mataki na ci gaban tattalin arzikin al’ummarta, ta hanya mafi saukin isa ga natija. A bayyane yake karara cewa ma’aikatar ayyuka ta Jihar Zamfara ba ta yi kasa a gwiwa ba, na ganin nasarar wannan gagarumin aiki ta dukkan fuskoki. Ta wannan hanya ce gwamnatin Abdul’aziz ke alfahari da shirye-shiryenta na bunkasa sashen manyan ayyuka, musamman hade gwadabun sassan jihar da tituna masu inganci domin kusanto da cibiyoyin kasuwanci zuwa ga mutane, wanda hakan ba shakka shi ne matakin farko na bunkasa tattalin arzikin al’umma.
Da yawan manazarta sun hadu a kan cewa lallai kafin zuwan wannan gwamnati ta Shehi (Abdul’aziz) a Zamfara, jihar ta kama hanyar tabarbarewa ne tun bayan kirkiro ta a 1996 kuma a ’yan shekarun baya, komai ya tsaya cik a kangarorin ayyukan raya kasa da al’umma. Babu abin da gwamnan ya gada illa kufai da abin da za a iya kira ‘jihar kauye’ a dukkan ma’anar kalmar; ga dai mummunan talauci wanda a fili yake kamar hasken rana. Sa’annan mutanen karkara suna sufurin amfanin gonarsu ta hanyar dorawa a kai, su tako a kasa zuwa garuruwa da kasuwanni, wasu kuma su dora a kan jaki saboda tsananin rashin hanya ko gwadaben da mota za ta iya ratsawa a tsakanin kauyuka da birane. Sai hakan ta haifar da tsaiko na kai da kawon mutane da amfanin gona a kasuwanni da garuruwa.
Gwamna Abdul’aziz Yari ya taka rawar gani sosai ta hanyar gaggauta bayar da kwangilolin gina tituna da za su hade da gwadabun birane da kauyuka a cikin kankanen lokaci. A wani jawabi nasa a yayin kaddamar da ayyukan hanyoyi a Jihar Zamfara, gwamnan cewa ya yi “…gwamnatina za ta tabbatar da cewa ta kammala dukkan ayyukan hanyoyi da gwamnatin da ta shude ta kasa kammalawa kafin fara sababbin ayyuka…” Hakan ta sanya gaggawar kammala mafi yawan kwangilar hanyoyin da Gwamnatin Shehi ta bayar a shekarar farko na hawansa tare da kaddamar da su a kan kari. Bugu da kari kuma sauran sabbin da aka bayar na biliyoyin nairori a duk fadin jihar, an sami nasarar kammala su tare da kaddamar da su a shekara ta biyu na mulkinsa. Sauran abin da ya rage kuma an kaddamar da su a jajibirin bikin cikar gwamnatinsa shekara uku a kan karagar mulki, illa dan abin da ba a rasa ba a nan da can.
Gwamnatin tasa ta aiwatar da manya-manyan ayyuka guda 32 a dukkan sassan jihar baki daya, wadanda suka hada da gina hanyoyi a garuruwan Anka, Gummi, Bukkuyum, Nasarawa Burkullu, Talata Mafara, Jangebe, Mori da sauransu da dama.
Akwai kuma hanyoyin garin Bakura, Maradun da takgwayen hanyoyin cikin garin Gusau. Ga tituna a Tsafe, Maru, dansadau, kaura Namoda, Zurmi, Moriki, Birnin Magaji, Shinkafi, Bungudu, Kwatarkwashi da sauran hanyoyi a dukkan garuruwa da sassan Jihar Zamfara.
Duka wadannan ayyuka na shimfida hanyar kwalta sama da kilomita dubu daya a cikin kankanin lokaci, an aiwatar da su ne a karkashin Ma’aikatar Ayyuka ta jiha, karkashin kwamishinanta Hon. Sharu D/Sarki Anka, wanda ya bayyana nasarorin ma’aikatar tasa a kan jajircewa da sadaukar da kan Gwamna Abdul’aziz Yari da kuma hadin kan al’ummar Jihar Zamfara. Ya kuma bayyana cewa ayyukan tituna a Jihar Zamfara na daga mafiya inganci da karko a duk fadin kasar nan, wanda hakan yana da alaka da sanya hazikan mutane masu gaskiya da kuma kamfanonin da suka goge a fannin aikin. Sa’annan kuma ya bayyana cewar gwamnatin ta kashe fiye da Naira biliyan 60 domin wannan aiki, ta kuma biya dukkan wadanda ke da ruwa da tsaki a aikin.
Babu shakka, daukaka matsayi tare da inganta tsarin sufuri a cikin kowace al’umma yana da tasirin gaske a bangaren ci gaban siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al’umma; don haka, ya dace a yi la’akari da hakan a matakan kananan hukumomi, yankuna da kuma tarayya. Matukar aka rasa kyawawan hanyoyi a cikin al’umma, to zai yi wahala al’ummar ta iya magance wa kanta matsalolin da suke addabarta. Don haka, irin wannan namijin aiki na Gwamna A. A. Yari zai zama madubi kuma abin koyi ga dukkan gwamnatocin da ke da kyakkyawar manufa na ci gaban al’ummominsu a dukkan fadin Najeriya.