Ko akwai darasi daga ambaliyar 2012?
Masu kula da dam din Lagdo da ke kasar Kamaru a kwanakin baya sun sanar da Gwamnatin Tarayya cewa za su sako ruwa kadan-kadan daga dam din domin kubutar da shi daga fashewa.Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ce da wasu ma’aikatu suka sanar da ’yan Najeriya wannan bayani, wanda yake jawo firgici da tashin […]
Masu kula da dam din Lagdo da ke kasar Kamaru a kwanakin baya sun sanar da Gwamnatin Tarayya cewa za su sako ruwa kadan-kadan daga dam din domin kubutar da shi daga fashewa.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ce da wasu ma’aikatu suka sanar da ’yan Najeriya wannan bayani, wanda yake jawo firgici da tashin hankali a jihohin da suka sha wahala a shekarar 2012 lokacin da mahukuntan wannan dam suka sako ruwa ba tare da gargadi ga Najeriya kan illar da ruwan zai haifar ga Najeriya.
A shekarar 2012 ne aka sako ruwa daga dam din kuma ya jawo ambaliya da aka ce ba a taba ganin irinta ba a shekara 40 a muni. Ambaliyar ta shafi jihohi 30 daga cikin jihohi 36 na kasar nan, kuma an kiyasta ta shafi mutum miliyan 17 tare da hallaka mutum 363 da raba mutum miliyan biyu da dubu 200, kuma ambaliyar ta jawo asarar dukiya da ta kai ta Naira tiriliyan biyu da biliyan 600.
Domin rage radadin illa da asarar da aka yi tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya saki Naira biliyan 17 da miliyan 600 ga jihohi da hukumomi domin kai dauki ga barnar da aka samu da bayar da tallafi da sake tsugunarwa.
Goodluck Jonathan ya kira ambaliyar da “Annoba ta kasa,” inda ya kafa Kwamitin Shugaban kasa kan Bayar da Tallafin Ambaliya da Sake Tsugunarwa. Kwamitin mai shugabannin hadin gwiwa biyu na karkashin mai kudin Afirka Aliko Dangote da dan rajin kare hakkin jama’a, Olisa Agbakoba (SAN).
Kwamitin ya tara sama da Naira biliyan 17 kudi da alkawari kuma ya kammala aikinsa a shekarar 2014 ba tare da sake tsugunar da wadanda ambaliyar ta shafa ba.
Kudin da aka ba jihohi daga Gwamnatin Tarayya an sarrafa su tamkar wata ganima domin shaidu sun nuna cewa an karkatar da kudin kuma ba jihar da ta kwashe jama’a daga wuraren da suke fuskantar ambaliyar.
Jihohin sun kare ne da raba wa wadanda ambaliyar ta shafa Naira dubu bibbiyu zuwa dubu uku-uku da dari biyar, yayin da ba a cika alkawarin sauya musu matsuguni ba. Bayan ambaliyar 2012 Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) da ta hasashen yanayi sun ce an gargadi gwamnonin jihohi kafin aukuwar annobar amma suka ki daukar mataki.
Wata ambaliyar ta fara kuma lura da yadda gwamnatocin jihohi da na tarayya suke rikon lamarin ya nuna cewa ba mu dauki wani darasi daga abin da ya faru a shekarar 2012.
Ba a musayar bayanai yadda ya kamata a tsakanin hukumomin gwamnati da suke kula da hasashen yanayi. Sanarwar alamun aukuwar annoba da Ma’aikatar Muhalli take bayarwa a mako-mako an dakatar da shi bisa umarnin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya saboda korafi daga Hukumar NIMET.
Hukumar Kula da Ruwan sama, The Nigeria Hydrological Serbice Agency a hasasehnta na bana mai taken: 2015 ‘Annual Flood Outlook,’ ta yi hasashin cewa jihohi 12 za su samu ambaliyar ruwa sosai a bana, amma wadannan jihohi aka shammace su, ambaliya ta fara kafin ma a sako ruwa daga daga dam din Lagdo wanda ya kashe mutane da dama da rusa gidaje da gonaki da lalata dukiya.
Ya kamata a ce Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta giggina kananan dam-dam don rage illar da sako ruwa daga dam din Lagdo ke tun daga shekarar 2012, amma hakan bai yiwu ba.
Jama’a na dora laifin ambaliyar ne a kan gwamnati saboda ta mance da nauyin da ke kanta.
kididdiga ta baya-bayan nan daga Ma’aikatar Kula da Muhalli ta nuna abubuwan da mutane suke yi ke jawo kashi 60 cikin 100 na ambaliyar da take shafarsu. Ya zame al’ada ga jama’a su rika zuba shara a magudanun ruwa da gina gidaje a kan hanyoyin ruwa a wasu wuraren ma babu magudanun ruwan kacokan balle ruwan ya samu hanyar wucewa da damina.
Wani taron gaggawa na ma’aikatu da hukumomi kan yawaitar ambaliyar ruwa da aka gudanar kwanakin baya ya ba da wasu shawarwari kan matakan da za a dauka don rage illar da ambaliyar ke haifarwa, kuma daya daga cikin abubuwan da aka ambata shi ne a sanya kwamitin su Dangote ya bayyana rahotonsa ga jama’a.
Batun da ke gabanmu ya tsallake na bayyana rahoton ga jama’a, abin da ya faru da Naira biliyan 17 da kwamitin ya tara tukun, kuma a binciki yadda jihohi suka yi da Naira biliyan 17 da aka ba su tallafi kan ambaliyar daga Gwamnatin Tarayya.
Kuma wajibi ne jihohi su dauki matakan tilasta bin dokokin yin gine-gine da na tsara garuruwa da suke hana mutane yin gine-gine a hanoyin ruwa, kuma a fadakar da jama’a illolin da ke cikin zuwa shara a magudanun ruwa.
Wajibi ne gwamnati ta bullo da wani tsararren shiri da zai kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa gaba daya tunda sauyawar yanayi tana nuna alamun aukuwar hakan.