Ko akwai son kai da bangaranci a nadin mukaman Gwamnatin Buhari?

An samu wasu na korafin cewa Shugaban kasa ya nuna bangaranci da son kai wajen nade-naden mukamai a gwamnatinsa, inda suke nuna cewa ya fi ba ’yan Arewa muhimmanci. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko akwai gaskiya cikin wannan batu kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: […]

Ko akwai son kai da bangaranci a nadin mukaman Gwamnatin Buhari?
Ko akwai son kai da bangaranci a nadin mukaman Gwamnatin Buhari?

An samu wasu na korafin cewa Shugaban kasa ya nuna bangaranci da son kai wajen nade-naden mukamai a gwamnatinsa, inda suke nuna cewa ya fi ba ’yan Arewa muhimmanci. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko akwai gaskiya cikin wannan batu kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Babu son kai a Gwamnatin Buhari – Jibrin Abdullahi

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Jibrin Abdullahi (Jibo): “Gaskiya abin da na lura da salon mulkin Muhammadu Burahi shi ne, ba ya nuna son kai ko kuma wariya ga nade-nadensa. Idan mun lura sosai, shi Buhari, kowa nasa ne a kasar nan, alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, yana aiwatar da su bisa dacewa. Idan mun duba yadda ya nada ministoci, bai saba wa ka’idar tsarin mulki ba, ko a batun ministoci, ya nada su bisa cancanta kuma sun fito daga dukkan sassan kasar nan. Don haka babu batun cewa wai ya fi nada ’yan Arewa a mukamai, domin kuwa shi kasar yake wa aiki gaba daya ba wani sashi ba. Babban aikin da ya sanya gaba shi ne yaki da almundahana kuma duk wanda ya taba dukiyar gwamnati ana taba shi koda daga wane sashi ko kabila ko addini ya fito a kasar nan. Don haka, masu zargin Buhari cewa yana son kai, su ji tsoron Allah su daina, domin kuwa shi gyara yake ba tare da sani ko sabo ba.”

 

Batun son kai ba haka ba ne – Abdullahi Yahaya

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Abdullahi Yahaya: “Batun cewa Shugaba Buhari yana nuna son kai a nade-nadensa, wannan ba haka ba ne; domin kuwa abubuwansa yana aiwatar da su ne daidai bisa adalci. Kuma mu fahimta da wani abu da mulkin siyasa shi ne, wanda ya yi maka aiki, shi za ka fara dubawa. Idan ma ana zargin ya maida hankali kan wani sashi, babu mamaki su ne suka yi masa hidima, suka zabe shi. A lokacin mulkin Jonathan, babu abin da ba a yi ba. Akan cire dan Arewa a wani mukami, a maye gurbinsa da dan Kudu, amma babu wanda ya koka cewa ya yi son kai, sai yanzu ne don dan Arewa na mulki. Ke nan shi dan Arewa duk abin da ya yi bai iya ba, sai an kushe shi? Don haka Gwamnatin Buhari a daidai take tafiya, babu son kai ko wariya. Idan ana son a gane haka, a duba baya, yadda gwamnatin baya ta tafiyar da mulkinta.”

 

Ban ga kuskure a
nade-naden Buhari ba
– Umar Gabari

Abubakar AbdurRahaman Dodo, a Kano

Umar Musa Gabari: “Idan muka yi la’akari da cewa shugabanci amana ce da al’umma ke danka wa mutum kuma Allah Ya tabbatar da ita bisa umarnin yin adalci ga kowa da kowa, sai mu ce babu kuskure a nade-nade mukaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi. Duk mai mulki adali da ke son sauke amana da nauyin al’umma da Allah Ya dora masa, wajibi ne ya nemi mutanen da za su taimaka masa. Irin wadannan mataimaka dole su kasance adalai. Ta yiwu wannan ne dalilin Shugaba Muhammadu Buhari wajen zaben wadanda ya sani, ko ya san su ciki da waje, don su tallafa masa wajen gudanar da harkokin mulki. Kuma ai mulkin da aka yi a baya tun daga na Shugaba Obasanjo zuwa Goodluck babu wanda bai fifita ’yan yankin sa ba.”

 

Nade-naden Buhari babu son rai a cikin su – Ali Ibrahim

Abubakar AbdurRahaman Dodo, a Kano

Ali Ibrahim Sani Mainagge: “A ganina bai kamata a ce Shugaba Buhari ya yi son kai, ko ya fi son ’yan bangarensa ba. Gwamnatocin baya ma sun kwata irin wannan, don haka ba sabon abu ba ne. Shugaba ’Yar’aduwa daukacin harkokin kudin kasar nan a hannun ’yan Jihar Kano ya danka amanarsu. Tun da wannan al’amari ba sabon al’amari ba ne, abin da ya kamata ’yan adawa su mayar da hankali a kai, shi ne cancantar wanda aka nada bisa kowane irin mukami; yaya kwarewarsa za ta yi tasiri wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar nan, ba tare da la’akari da bangaren da suka fito ba, ko kabilarsu ko addininsu. Da ’yan siyasa da ke nuna adawa game da slaon mulkin shugaba sun san cancanta ce ta fi komai, watakila ba za su bata lokacinsu wajen cewa an fifita wani bangare, a kan sauran sassan kasar nan ba.”

 

Ban ga son zuciya ga Buhari ba – Salisu Yarima

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Muhammed Salisu Yarima: Wannan magana da wasu ke yi ba gaskiya ba ce, domin Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne da ke aiki da doka da oda kuma duk mutumin da zai ba shi mukami sai ya yi bincike a kansa ya gano mutum ne mai gaskiya da rikon amana. Ina so mutane su fahimci cewa mutanen Arewacin kasar nan sun fi kamanta adalci fiye da ’yan kudanci, lokacin da Shugaba Goodluck Jonathan yake mulki, kusan dukkan jami’an tsaron kasar nan manya ’yan kudancin kasar nan ne kuma babu wani dan Arewa da ya yi korafi ta kafafen watsa labarai.
Kuma su fahimci cewa mutanen Arewacin kasar nan sun fi su yawa. Akwai mutum daya mai ’ya’ya 40 ko 30 ko 20 zuwa kasa, duk da haka babu wata jiha da Shugaba Buhari bai ba ta mukamin minista ba amma saboda son zuciya sun gagara fahimtar haka.

 

Ba wariya a mukaman Buhari
– Nasiru Aminu

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Adamu Nuhu ’Yan Kwada: “Idan an ba su fansho da garatuti, mu kuma masu zabe a ba mu nawa? Biyan ’yan majalisu wani alawas ma bayan kammala shekara hudu rashin adalci ne. Da a yi haka gara a cika alkwarin da Baba Buhari shugaba ya yi; na biyan matasa da dattawa marasa galihu tallafin Naira dubu biyar, wanda su ’yan majalisun suka soke lokacin da aka gabatar a gabansu. Shi ma talakan da ya zabe su, sai ya karbi nasa garatutin da fansho ko? Maimakon a ba su su kadai.”