Ko amfani da katin zabe na dindindin a zaben 2015 zai yi tasiri?

Hukumar Zabe (INEC) ta kuduri aniyar yin amfani da katin zabe na dindindin a zaben badi, inda ta sha alwashin cewa duk wanda bai da katin ba za a bar shi ya yi zabe ba. Ganin irin kalubalen da ke fuskantar al’amarin, shin ko amfani da katin zai yi tasiri kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane […]

Ko amfani da katin zabe na dindindin a zaben 2015 zai yi tasiri?
Ko amfani da katin zabe na dindindin a zaben 2015 zai yi tasiri?

Hukumar Zabe (INEC) ta kuduri aniyar yin amfani da katin zabe na dindindin a zaben badi, inda ta sha alwashin cewa duk wanda bai da katin ba za a bar shi ya yi zabe ba. Ganin irin kalubalen da ke fuskantar al’amarin, shin ko amfani da katin zai yi tasiri kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Katin zai yi tasiri sosai – Auwal Suleiman

Musa Kutama, a Kalaba

Auwal Suleiman Muhammad: “A gaskiya amfani da katin zabe na dindindin ya dace domin zai yi maganin irin mutanen da ke yin zabe sama da sau daya, wanda muna sa rai yin hakan zai magance wannna badakala da kuma magudin zabe in sha Allahu. Don haka katin a zabe mai zuwa zai yi tasiri sosai.”

Katin ba zai yi wani tasiri ba – Malam Hassan

Malam Hassan Usman Zango: “A gaskiya babbar matsalarmu a kasar nan ita ce yadda hukumomi suke yaudarar al’umma. Batun katin zabe, ina tabbatar maka da cewa ba zai yi wani tasiri ba a zaben 2015 da muke tunkara; domin da yawa daga cikin wadanda suka yi rijistar amma kadan daga cikinsu ne suka samu katinsu na dindindin. Muna ganin hukumomi suna so su yi amfani da matsalar katin domin yin magudin zabe. Misali, ni har yanzu ban samu nawa katin ba kuma a mazabarmu sama da mutum 2000 sun yi rijista amma mutum 800 ne suka samu katinsu.

Akwai matsala a wannan katin – Abubakar

Abubakar Ba Matsala: “A ra’ayina, wanann kati ba zai yi tasiri a zabe mai zuwa ba, kasancewar ba kowane mutum ne ya samu katin ba. Matsalolin da aka samu a yayin gudanar da wanann aikin sun faru ne da niyya, domin ana sane aka yi hakan. Ba a so mutane su yi zabe shi ya sa. Idan an duba, a cikin kashi uku na mutanen da suka cancanci yin zabe, kashi daya ne rak suka samu wanann kati. Ka ga idan har aka ce sai da wanann kati za a yi zabe, to ina tabbatar da cewa zabe ba zai yiwu yadda ya kamata ba.

Katin dindindin zai biya bukata – A’ishatu Ayuba

Musa Kutama, a Kalaba

A’ishatu Ayuba Mshelia: “Gaskiya a nawa ra’ayin da kuma fahimta, ya dace a ci gaba da yin amfani da katin dindindin na zabe, ba don komai ba sai don nuna tabbacin mutum dan kasa nagari ne mai kuma kishin kasarsa. Har wayau kuma karin tabbaci ne na mutum ya kai munzalin yin zabe a kasarsa. Amfani da katin zai kara wa duk dan kasa kwarin gwiwa; don haka zai biya bukata sosai.”

Katin zai taimaka a yi magudi – Musa Aliyu

Hamza Aliyu, a Bauchi

Malam Musa Aliyu Jahun: “Kamar yadda kowa ya sani, saura watanni kadan a gudanar da babban zaben shekara ta 2015 kuma tabbas hukumar zabe ta ce babu wanda zai jefa kuri’a sai yana da sabon katin da ta raba. Na biyu ya kamata hukumar zabe ta fahimci cewa da yawa daga cikin wadanda suka yi rijista sun ga sunayensu a rumfunar zabe amma ba su samu katinsu, ba sannan kuma akwai wadanda babu sunayensu babu hotunansu don haka muke zargin watakila akwai wani shiri da hukumomi suke yi domin tafka magudin zabe. Idan aka ce babu wanda zai kada kuri’arsa sai yana da katin to tabbas hukumar zabe ta INEC ta shirya wani magudi a karkashin kasa.

Katin ba zai yi tasiri ba – Sirajo Umar

Lubabatu I. Garba

Sirajo Umar: “Maganar a ce kati zai yi tasiri a zaben 2015 ma ba ta taso ba, domin wanann aiki bai samu kowace irin nasara wajen gudanar da shi ba. Kodayake ana ganin jam’iyya mai mulki ce ta shirya hakan, don ganin talakwa wadanda su ne suka fi zuwa kada kuri’a a lokacin zabe ba su kai ga samun katin ba. Dalilinsu na yin hakan ba a boye yake ba, wadannan talakwa duk jama’a ce ta jam’iyyar adawa wacce ake hangen za ta sami nasara a zabe mai zuwa don haka aka ki shirya abubuwan da suka kamata don gudanar da aikin raba katin rajistar.