Ko azumi na iya kara lafiya?

Wadansu za su yi mamaki idan suka ji cewa a yanzu haka likitoci a fadin duniya har a kasashen da babu addini sosai, suna iya rubuta wa mutum azumi domin kiyayewa ko magance wasu matsaloli na rashin lafiya. Wato maimakon su ba mutum magani, sai su ba shi shawara cewa ya rika azumi, kamar yadda […]

Ko azumi na iya kara lafiya?

Ko azumi na iya kara lafiya?

Wadansu za su yi mamaki idan suka ji cewa a yanzu haka likitoci a fadin duniya har a kasashen da babu addini sosai, suna iya rubuta wa mutum azumi domin kiyayewa ko magance wasu matsaloli na rashin lafiya.

Wato maimakon su ba mutum magani, sai su ba shi shawara cewa ya rika azumi, kamar yadda wasunsu kan ce mutum ya rika yawan motsa jiki. Irin azumin da likitocin zamanin nan suka fi rubutawa shi ne irin azumin Annabi Dawud (AS), wato mutum ya yi azumi yau, gobe ya sha, wanda a likitance suke kira Intermittent Fasting. Kai wasunsu ma suna ba da irin na wata cikakke ko ma sama da haka a jere. Wato duniyar likitanci sai a ’yan wadannan shekaru ne ta gano amfanin azumi ga lafiya. Idan mutum yana son karin bayani a kan wannan maudu’i da ganin irin cututtukan da akan rubuta wa irin wannan azumi, sai ya sa wadannan kalmomi a Intanet domin bahasi. Bari mu duba irin alfanun nasa ga lafiyarmu.

Da farko dai azumi na daya daga cikin hanyoyin gyara lafiyar jiki da ta tunani wato lafiyar kwakwalwa, domin binciken kimiyya ya tabbatar a wasu lokuta ciki da hanji sukan bukaci hutu daga kowane irin abinci na wani dan lokaci. Hakan kan sa kitsen jiki ya narke, sinadarai da guba da hanta ta tara kuma su kone. Jiki kan narka kitse ne ta hanyar amfani da shi a matsayin abinci. Wannan kan sa mutum ya dan sabe.

Ban da tacewa da kona guba, har ila yau hanta kan fito da abincin da ta tara (irin su sinadaran glycogen da fatty acid na kitse) don jiki ya sarrafa su zuwa sukari wanda yake ba da kuzari na dan wani lokaci don amfanin jiki, domin ita hantar ta fara shirin ajiye sabo. Wannan ma kadai kan kara lafiyar hanta. Bayan hanta shi ma hanji yakan samu ya dan huta na wani lokaci ya daina kumburi ko cushewa da yake yawan yi a wasu mutanen musamman irin masu cututtukan hanji daban-daban.

Masu yin azumi suna cike da tunani na annashuwa domin hasashen lada na aikin ibada, wanda wannan annashuwa kadai wani karin lafiya ne ga tunani da aikin kwakwalwa. Wannan ne ya sa masana ke ganin azumi zai iya tasiri akan ciwon damuwa na depression, da ciwon gajiyar yau da kullum wato stress.

Wadansu za su ce ai duk jiki zai iya samun wadannan ba tare da azumi ba, sai masana kimiyya suka ce, eh haka ne amma domin mene ne  ko a wurin gwaje-gwaje na asibiti wurin auna sukari da maikon jini da wasu sinadaran jiki akan ce mutum sai ya yi azumin akalla awa takwas kafin a auna su. Domin a lokacin ne jiki ke nuna sinadarai na hakika ba na zukale ba. Haka ma dole wanda za a yi wa wata babbar tiyatar aiki ta jiki, ko ba ta hanji ba, a ce ya yi azumi kafin tiyatar saboda a lokacin jiki ya samu ya huta daga duk wata hayaniyar yau da kullum.

Yawan azumi zai iya zama kariya da magani ga ciwon hawan jini.

Kamar yadda binciken masana da dama ya nuna, ciwon hawan jini kan saisaitu sosai a wasu mutanen yayin da suke azumi. Misali wani likita dan kasar Amurka mai suna Dokta Goldhamer wanda ya kware a bincike kan azumi ya yi nazarin amfanin azumi ga masu hawan jini. A cikin mutane masu hawan jini da ya gwada yayin da suke yin azumi, kashi 98 cikin 100 ba su bukaci magungunansu ba a tsawon ranakun da suka dauka suna azumi, wato azumi kawai ya saisaita hawan jinin nasu.

Wannan bincike ba ya nufin mutum mai hawan jini don ya dauki azumi sai ya ajiye magani ba ne, a’a sai idan likitansa ne ya auna ya ce ya huta.

Zai kuma iya zama kariya daga ciwon suga. Su kansu masu ciwon suga, azumi kan saisaita yawan sugar jikinsu, sai dai akan shawarce su da su rika yin amfani da na’urar auna suga a kullum saboda sugar za ta iya yin kasa sosai su galabaita. Sai dai ana so mai ciwon suga mai amfani da allurar insulin ya shawarci likitan da ke ganinsa ko zai iya daukar azumi, sa’annan ya yi tambaya a kan ta yaya zai saisaita allurar saboda bambancin lokacin cin abinci.

Ga masu shan miyagun kwayoyi da taba sigari, azumi na daya daga cikin hanyar horar da kwakwalwa barin sabo da su, wato barin nacin begen abin shan (addiction). Wato azumi zai iya maganin addiction tunda azumi na tarbiyyantar da jiki da kwakwalwa a kan kore begen ko ma mene ne mutum ke tu’ammali da shi. Ga mai so ya daina wannan dabi’a, azumi zai iya taimakonsa kwarai da gaske.

Yawan azumi kariya ne daga cututtuka da sukan faru dalilin borin jiki (inflammation)irin su sanyin kashi da sauransu. Masana suka kara da cewa ban da irin wadannan cututtuka azumi har kiyaye cututtukan daji zai iya yi, saboda shi ma daji sanadinsa shi ne borin jiki. Haka nan sun kara da cewa yawan azumi a kuruciya yana iya rage kaifin tsufa da alamominsa wato irin tamojin nan da tattarewar fata ta tsufa.

Sai dai akwai kuma wasu larurori na rashin lafiya wadanda a addinance ba a dora wa masu su azumi ba. Wadannan sun hada da marasa lafiyar da sai an kwantar an tayar ko wadanda ba su san halin da suke ciki ba, ko wadanda suke kwance ake yi wa karin ruwa, ko jini, da masu gyambon ciki na olsa wadanda rashin shigar abinci cikinsu kuma kan iya tayar musu da ciwon da dai sauran ire-irensu. Masu juna biyu ko masu shayarwa su ma akan yi musu sauki. Masu irin wadannan larurori suna kuma bukatar fatawoyin malamai, bayan shawarwarin  likitoci, don a tabbatar musu za su iya azumi ko akasin haka da kuma hanyoyin ramuwa ko kaffara.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna