Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa?
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:
Binciken yana yin tasiri – Yahaya Usman
Hussaini Yahaya Usman: “A fahimta ta, shingayen binciken suna rage ayyukan ta’addanci da kuma barazanar tsaron da kasar nan ke fuskanta. Kasancewar jami’an tsaro a wuraren na taimakawa wajen rage ayyukan miyagu saboda a lokuta da dama hakan kan jefa tsoro a zukatan wasu masu mugun nufi ga al’umma. Duk da cewa shingayen na haifar da tsaiko da kuma cinkoson ababan hawa, wanda hakan ke kara tsawon lokacin tafiya. Amma a nawa ra’ayin suna tasiri wajen samar da tsaro.”