Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 1

Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]

Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 1
Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 1

Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:

Shingayen ba su da tasiri – Yusuf Abdullahi

Yusuf Abdullahi: “A gaskiya a ganina, wadannan shingayen binciken ba su da wani amfani saboda har yanzu ba mu taba ji an ce a wajen ga wani mutum da wani jami’in tsaro ya cafke da makami ko wani abin da bai dace ba. Ka ga ke nan ba su da amfani saboda haka a cire su shi ya fi. Kuma idan ka duba da kyau, wuraren da aka kafa shingayen nan, wurare ne da a yanzu jami’an tsaro ke samun damar tsare masu ababan hawa don karbar cin hanci daga gare su. Samar da ayyuka ga matasa shi ne babban abin da gwamnati ya kamata ta sa a gaba, amma ba kafa shingayen bincike ba.”