Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 2
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:
Binciken ba ya da tasiri – Abubakar Ibrahim
Abubakar Ibrahim Ustaz: “A matsayina na direba mai bin hanyoyi a nan cikin birnin Kano, tun da nake ban taba jin cewa an kama wani mai laifi a wajen buda ababen hawa ba, sai dai ma kawai a hada cunkoso amma a kwanakin nan da aka dauke wadannan wuraren; ai ga shi an samu saukin cunkoso a kan hanyoyinmu. Ni dai ban taba ji ba kuma ban taba gani an kama mai laifi a wajen ba kuma kamata ya yi idan an gano mai laifin a ce a nan take a ga an kama shi, amma ban taba ganin hakan ba. Kuma duk ma’aikaci ya san ta inda zai gano mai yin laifi, ba wai sai a wajen tare ababen hawa ba. Inda ma ya kamata a rika wannan binciken kamata ya yi a ce a hanyoyin wajen gari ne amma ba a cikin gari ba. Amma a cikin gari inda mutum yana sauri zai je wajen aiki ko kasuwa ko wani waje muhimmi, wannan binciken yana kawo cikas da takura wa mutane.”