Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 3
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:
Bincike ba ya maganin komai – Bashir Abubakar
Alhaji Bashir Abubakar: “A hakikanin gaskiya wannan ba ya maganin matsalar tsaro. domin kuwa tsare mutane da ake yi a kan hanyoyi ba shi ne zai tabbatar da kyakkyawan tsaro a Najeriya ba. Kamar yadda ’yan sanda suke tsare hanya wani lokacin sai ka ga sai an yi kewaye ta wasu hanyoyin, wannan yana takura wa mutane. Don haka ni a ganina cire wadannan wuraren duba abin hawa shi ne mafi alheri, domin su ’yan sand sun fi kowa sanin inda bata-gari suke da kuma inda za a kama su, ba wai mutanen gari ba ne za su binciko su. Ni a ganina ai ba a kasuwa ko a kan titi ake gane mai laifi ba. Na farko dai a duba wajen shiga gari na waje, ba wai mahada ta cikin gari ba.”