Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 4
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:
Aikin tsaron ba ya tasiri – Alhaji Audu
Alhaji Audu G.G. “Abin da na lura dangane da abin da sojoji suke yi a kan hanyoyin kasar nan da sunan neman zakulo miyagun mutane, a gaskiya babu wani abin a zo a gani da za a ce sojojin suke tabukawa illa kawai irin abin da ake cewa da babu gara ba dadi, amma in ba haka ba sai in ce kafa shingayen nasu kamar kara tunzura masu aikata barna ne kurum a yankunan da ake cikin fitintunu. Dalilina kuwa shi ne, domin su wadannan sojojin akwai gurbatattu a cikinsu don haka da wahala a ce al’ummar kasar nan suna gamsuwa da abin da suke yi na binciken ababen hawa a kan hanyoyin kasar nan ko cikin birane inda ake fama da matsalar tashe-tashen hankula. Don haka shawarar da zan bayar, idan saboda tsaro ne gwamnatin take tura su, ya kamata manyansu su sa musu ido a duk inda suka kai su aikin tsaron jama’a.”