Ko binciken da sojoji ke yi a shingayen hanyoyi yana tasiri kuwa? 5
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su […]
Kowa dai yana sane da irin yadda shingayen bincike a hanyoyin kasar nan, musamman ma a Arewa suka zama ruwan dare, inda sojoji ke binciken ababen hawa, musamman da nufin magance matsalar tsaro da ta addabi al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin irin wadannan bincike-bincike ko suna yin tasiri kuwa ko ba su yi? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban kamar haka:
Kadan ne tasirinsa – Magaji Sama’ila
Alhaji Magaji Suma’ila: “Lallai ni abin da nake gani gaskiyar maganar ita ce, sha’anin Sojoji masu bincike a kan hanyoyin kasar nan suna da amfani amma ba sosai ba ne, domin sau tari ake samu a wuraren da suke yin binceken ne miyagu mutane masu aikata barna suka fi cin karensu ba tare da babbaka ba. Misali, idan aka yi la’akari da irin wasu yankuna na sassan jihohin Arewa da suke fama da tashin-tashina na siyasa ko addini, wanda ya sa da dama mutane suke kallon aikin sojojin tamkar yaudara ce kurum. Domin binciken da suke yi din bai hana ci gaba da fashi da makami ko a ce ya dakatar da masu kai hare-hare a kan jama’a ba amma kuma da yake suna fitowa ne da sunan masu tsaron kasa, to ya wajaba da su zage damtse su yi aiki na kare lafiya da rayukan jama’a. Wannan ita ce gaskiyar maganar kuma mai sa mutane su yarda da cewa wadannan sojojin suna yin aiki domin tsaro kuma binciken da suke yi zai tabbatar da gaskiya.”