Ko cire shingayen hanya da gwamnati ta yi ya dace

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire dukkan shingayen bincike na sojoji daga titunan Najeriya, ban da na Jihohin Arewa Maso Gabas, inda ake da matsalar Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko cire shingayen ya dace kuwa? Ga abin da mabambantan jama’a ke cewa: Cire shingayen […]

Ko cire shingayen hanya da gwamnati ta yi ya dace
Ko cire shingayen hanya da gwamnati ta yi ya dace

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire dukkan shingayen bincike na sojoji daga titunan Najeriya, ban da na Jihohin Arewa Maso Gabas, inda ake da matsalar Boko Haram. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko cire shingayen ya dace kuwa? Ga abin da mabambantan jama’a ke cewa:

Cire shingayen ya yi daidai- Muhammad Bara’u

Musa Kutama, a Kalaba

Muhammad Bara’u: “Janye shingaye daga kan hanyoyi da gwamnati ta yi, a gaskiya ta yi mini daidai domin irin yadda jami’an tsaro ke faman takura wa jama’a da ci masu mutunci kan kudi kalilan a wasu lokutan ma har da fasinjoji. Rannan muna dawowa daga Aba har sai da wani jami’in tsaro ya so ya jawo mana hadari, ya karbe makullin direba motar mu taso fadawa rami a kan kudi da ba su wuce Naira 50 ba. Janyewar ta yi maganin karbar na goro da wulakanta mutane da jami’an tsaro ke yi.”

Cire shingayen alheri ne- Auwal Suleiman

Madalla da cire shingayen- Sadik Adamu

Rabilu Abubakar, a Gombe

Sadik Adamu: “Cire shingayen kan hanya ya yi daidai, domin kamata ya yi a ce sojoji suna jeji ne ko fagen daga ba tsayuwa a kan hanya suna karbar goma ashirin ba. Babu abun da wadannan shingaye ke haifarwa sai koma baya, domin sukan haifar da tsaiko ga matafiya wajen yin amfani da wannan shingaye suna tauye wa matafiya da direbo hakki. Sojoji da ’yan sanda su gane fa Shugaban kasa Buhari yana so ya dawo musu da darajarsu ne da kuma ba su dama su dawo barikokinsu, kusa da iyalansu ya sa aka cire wadannan shingaye.”

Cire Shingayen abu ne mai kyau – Kabir Magaji

Rabilu Abubakar, a Gombe

Muhammad Kabir Magaji: “Cire shingayen kan hanya da Shugaban kasa ya ce a yi, ya yi mana kyau musammam ma mu direbobi da mu abun ya fi shafa. Mu direbobi daga lokacin da muka ji an ce a cire duk wani shingen kan hanya na jami’an tsaro, muka ji kamar don mu aka yi domin wadannan shingaye suna yi mana tarnaki. Tafiyar da ba ta wuce ta sa’a uku ba sai ta zama ta sa’a biyar ko shida.
“Na jinjina wa Shugaban kasa Muham-mad Buhari kan wannan al’amari. Ina neman kuma da a samar da tsaro mai inganci a kasar nan don gudun kar barayi su sami yadda suke so wajen yi wa direbobi fashi da makami, ganin an cire shingayen.”

Cire sojojin ya fi- Bello Rahusa

Muhammad Yaba, a Kaduna

Malam Bello Idris Rahusa: “Janye shingen ya dace domin dama ba abin da sojojin ke yi a kan titi sai matsa wa mutane da masu ababen hawa a kan hanya babu gaira babu dalili. Da yawan lokuta idan ka samu kanka a kan hanya kusa da wadannan shingaye a cikin mota, akan dauki lokaci ana bin layi ba tare da binciken komai ba, sannan suna cutar da jama’a. Wannan ya sa nake ganin janye shingen sojojin a kan titi zai taimaka, domin a yanzu musamman a Jihar Kaduna mun fara samun walwala saboda babu sojoji a kan titi.”

Gwamma da aka cire su – Aliyu Muhammad

Muhammad Yaba, a Kaduna

Aliyu Muhammad: “Gwamma da aka cire su daga kan titi, domin dama kwata-kwata ba su da amfani. Domin dai sojojin ba su iya hana wucewa da makamai a kan titi, ba su binciken komai. Dama can duk wani cunkoso da ake yi a kan titi, duk su ke janyo hakan. Saboda haka cire su a wajena ya fi zamansu a kan titi.”