Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta?

A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]

Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta?
Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta?

A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:

Arzikin Najeriya ya inganta – Zayyana Mamman

Zayyana Mamman Mai Walda Malumfashi: “Babu shakka tattalin arzikin Najeriya ya inganta, abin da kawai muka rasa shi ne ingantaccen shugabanci. Ga dalilaina na fadin haka: Idan ka duba bangaren ilimin zamani da na addini, an samu ci gaba a kasar nan ta yadda za ka ga maza da mata, yara da manya kowa ya dage neman ilimi. Idan ka duba zamantakewa, an samu wayewar kan al’umma ta yadda ba a fada da juna. Ta fuskar tattalin arziki kuwa, nan ma sai son barka, domin za ka ga maza da mata, yara da manya ana ta sana’a da neman arziki. Ta fuskar siyasa kuma, nan ma kai ya waye, mutane na zaben ’yan takarar da za su yi musu aiki ne. Saboda haka, idan ka duba wadannan sassa, za ka ga cewa karuwar arziki ne ya kawo bunkasa da wayewar kan al’umma. Abin da ya rage kawai shi ne, a samu shugabanci mai kyau, mai adalci.”