Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 0
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:
Bai inganta ba ko kadan – Nana Maigwanjo
Nana Maigwanjo: “Arzikin ya bunkasa ta fannin rashin kayan more rayuwa, rashin watar lantarki da asibiti da ilimi da kasha-kashen mutane da kwana da yunwa. Idan haka ne ai ka ga dole su ce arizikin kasa ya bunkasa a duniya ma ba a Afirika ba, na yarda mu ne na daya.”