Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 01
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:
Arzikin bai inganta ba – Khalid Imam
Khalid Imam: Wannan batu da ake yi na cewa tattalin arzikin Najeriya wai ya bunkasa, ni dai ban gani a kasa ba. A zamanin da talauci ya yi wa al’umma katutu, mutane babu walwala, babu wutar lantarki, babu ruwan sha, ana matsalar man fetur, sai kuma a rubuta wasu lambobi a takarda, sannan a ce arziki ya bunkasa? Idan ba haka ba, ana cewa wai arzikin namu har ya fi na Afirika Ta Kudu amma ko jirgin kasa ya gagare mu, shin yaushe za mu amince da wannan rahoton? Ga harkokin tsaro sun tabarbare, harkokin jirgin sama sun lalace, babu ingantattun hanyoyin sadarwa, yaushe za a ce mun fi wata kasa kamar Afirka Ta Kudu, wacce duk ta fi mu ingancin wadannan abubuwa. Ni dai a ganina, wannan rahoton wani salo ne na yaudara kurum, amma babu wani inganci a tattalin arzikin kasarmu.”