Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 02
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:
Ban amince da batun ba – Malam Isma’ila Madallah
Malam Isma’ila Abdullahi Madallah: “Najeriya dai kasarmu ce, ina da kuma kishin ta zamo zakara a komai amma a gaskiyar al’amari ni dai ban gani a kasa ba; watakila sai a gaba. A yanzu kam in band a karuwar tashe-tashen hankula da yawaitar rashin aikin yi da kuma karuwar talauci a tsakanin al’umma, ban ga wani abu da za a ce wai bunkasar tattalin arzikin kasa ba.”