Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 03

A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]

Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 03
Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 03

A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:

An samu karuwar matsala dai – Alhaji Yusuf

Alhaji Yusuf  dan’agwai Dakwa: “Bunkasar arzikin kasa da Najeriya ta ce ta samu abin farin ciki ne, sai dai abin da ke a zahiri, ni dai mu na nan koma bayan arziki muka gani da kuma karuwar matsalar rashin wutar lantarki, ga kuma layukan mai sai kuma yajin aikin makarantu. A rayuwata ban taba ganin munanan al’amura irin na wannan lokacin ba. Watakila a tsakaninsu su manyan gwamnati suke nufi, amma ga al’umma kam sai dai mu yi addu’ar Allah Ya musanya mana da mafi alheri; ba irin na wannan lokaci ba.”