Ko da gaske ne cewa karfin arzikin Najeriya ya inganta? 04
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske […]
A farkon makon nan ne al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani rahoto da ke nuna cewa karfin arzikin kasar nan ya bunkasa, ya inganta fiye da na sauran kasashen Afirika. Hakan na nufin cewa Najeriya ce ta daya a karfin arziki a dukkan nahiyar Afirika. Abin tambaya a nan shi ne, shin da gaske ne kuwa kasar da ’yan kasar sun azurta ko kuwa? Ga ra’ayoyin mutane nan daban-daban game da batun:
Arzikin manya ne ya inganta – Hajiya Hafsatu
Hajiya Hafsatu ’Yarbawa: « Arizikin Najriya ya bunkasa mana, amma a wajen manyan jami’an gwamnati, ba a Najeriya ko Afirika ba, domin kuwa za ka ga manyan gine-gine da manyan motoci a kan tituna kuma ana rasa rayuka wajen daukar matasa aiki; ga yawan kashe mutane da ake yi, ga yawaitar cin hanci da rashawa. Ai kuwa ka ga sun cce tattalin arzikin kasa ya bunkasa a wajensu, ba ga talakawan Najeriya ba. »