Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri?

Ila Maishayi Gbazango-Kubwa: “Wannan doka ta haramta shan taba a bainar jama’a, koda an zartar da ita ba za ta yi tasiri ba, domin kuwa su kansu wadanda suka kirkiro ta, su za su fara karya ta. Haka kuma, su mashaya sigarin ba za su dauki dokar da wani muhimmanci ba, domin sun san halin […]

Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri?
Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri?

Ila Maishayi Gbazango-Kubwa: “Wannan doka ta haramta shan taba a bainar jama’a, koda an zartar da ita ba za ta yi tasiri ba, domin kuwa su kansu wadanda suka kirkiro ta, su za su fara karya ta. Haka kuma, su mashaya sigarin ba za su dauki dokar da wani muhimmanci ba, domin sun san halin Najeriya. Ke nan ba za su daina shan tabar a bainar jama’a ba. Wani dalili kuma da ya sanya na ce dokar nan ba za ta yi tasiri ba shi ne, cin hanci da rashawa ya yi katutu a zukatan al’umma, tun daga sama har kasa. Ke nan, da kudi kadan sai mai laifi ya samu kansa daga hukuma. Wannan zai sanya babu wani tasiri da dokar nan za ta yi. Maimakon kirkiro dokar, da kamata ya yi gwamnati ta fuskanci wani abin mai muhimmanci da zai amfani al’umma, ba wannan ba.”

Babu abin da dokar za ta tsinana – Muhammadu Inda

Muhammadu Inda Tela Kubwa: “A ganina, dokar nan ba za ta yi tasiri ba, domin kuwa mashaya taba sigari ba za su iya dainawa ba domin dokar. Wannan dokar kuma za ta fi shafar talakawa masu karamin karfi ne kawai, wanda haka zai sa ba za ta yi tasiri ba, ganin cewa wani bangaren al’umma kawai za ta shafa. Wani abin lura kuma shi ne, wadanda za su aiwatar da dokar, wato jami’an tsaro, su ne ma kan gaba wajen shan tabar. Idan haka ne kuwa, to ta yaya mai dokar barci zai yi gyangyadi? Ai idan ka duba misali tabar wiwi ma, ai akwai doka mai karfi a game da shan ta, to an daina? Ba a daina ba, domin kuwa jami’an tsaro su ne kan gaba wajen shan ta da tu’ammali da masu sayar da ita.