Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 1
A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin […]
A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin shan ta a bainar jama’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan aka samar da dokar nan, ko za ta iya yin tasiri ga al’ummar Najeriya kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Dokar ba za ta yi tasiri ba – Ila Maishayi
Ila Maishayi Gbazango-Kubwa: “Wannan doka ta haramta shan taba a bainar jama’a, koda an zartar da ita ba za ta yi tasiri ba, domin kuwa su kansu wadanda suka kirkiro ta, su za su fara karya ta. Haka kuma, su mashaya sigarin ba za su dauki dokar da wani muhimmanci ba, domin sun san halin Najeriya. Ke nan ba za su daina shan tabar a bainar jama’a ba. Wani dalili kuma da ya sanya na ce dokar nan ba za ta yi tasiri ba shi ne, cin hanci da rashawa ya yi katutu a zukatan al’umma, tun daga sama har kasa. Ke nan, da kudi kadan sai mai laifi ya samu kansa daga hukuma. Wannan zai sanya babu wani tasiri da dokar nan za ta yi. Maimakon kirkiro dokar, da kamata ya yi gwamnati ta fuskanci wani abin mai muhimmanci da zai amfani al’umma, ba wannan ba.”