Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 2

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin […]

Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 2
Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 2

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin shan ta a bainar jama’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan aka samar da dokar nan, ko za ta iya yin tasiri ga al’ummar Najeriya kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Dokar za ta yi tasiri – Gambo Maicitta

Alhaji Gambo Maicitta: “A ganina dokar da Majalisar Zartarwa kasa ke kokarin kafawa kan masu shan sigari a cikin jam’a na hukuncin daurin watanni 6 ko tarar Naira dubu 50, a gaskiya dokar za ta yi tasiri matuka. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai dama abin da aka rasa ke nan, na kuma tabbatar da cewar in har hukumar ta daura damara a kan hakan, to kuwa za a kai ga nasara. Don haka ina fatan gwamnati za ta yi da gaske wajen kafa wannan doka kana ta kuma samar da daidaito wajen wannan doka ba tare da wariya ba.”