Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 3

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin […]

Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 3
Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 3

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin shan ta a bainar jama’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan aka samar da dokar nan, ko za ta iya yin tasiri ga al’ummar Najeriya kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Dokar ta yi daidai – Yusuf Potiskum

Dokta Yusuf Potiskum: “Ra’ayina dangane da wannan doka ta hana shan taba da Majalisar Zartarwa ke kokarin samarwa na hukuncin tarar Naira dubu 50 ko kuma daurin watanni shida ta yi daidai. Don a gaskiya in har an kafa wannan doka da kudiri mai kyau babu abin da zai hana ta karbu tare da samun goyon bayan jam’ar kasa. Don haka Allah Ya sa a kafa dokar a cikin nasara don ko shakka babu za ta yi matukar tasiri ga al’umma, domin kuwa za mu karbe ta hannu biyu-biyu.”