Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 4
A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin […]
A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin shan ta a bainar jama’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan aka samar da dokar nan, ko za ta iya yin tasiri ga al’ummar Najeriya kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ba lallai ne dokar ta yi tasira ba – Abubkar Abdullahi
Abubakar Abdullahi: “Da za a yi dokar ta yi tasiri da abin ya yi kyau, domin kuwa mutane da yawa suna shan tabar a bainar jama’a kuma babu damar a yi masu magana. Idan ka yi magana sai su ce ai ba kai ka ba su kudi ba; don haka ka rabu da su. Wannan ya sa nake ganin in da har hukuncin ko dokar ya tabbata a kasar nan za a magance matsalar shan taba a fili. Ina goyan bayan wannan hukunci sai dai ba lallai ba ne ya yi tasiri a Najeriya.”