Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 5

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin […]

Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 5
Ko dokar hana shan taba sigari a bainar jama’a za ta yi tasiri? 5

A kwanaki ne Majalisar Zartarwa Ta gwamnatin Tarayya ta shirya kudurin dokar hana shan taba a bainar jama’a, wanda za ta gabatar domin zartarwa a Majalisun Tarayya. Dokar dai, kamar yadda ake shirin zartar da ita, ta tanadi daurin wata shida ko tarar Naira dubu hamsin ga duk mashayin sigarin da aka samu da laifin shan ta a bainar jama’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan aka samar da dokar nan, ko za ta iya yin tasiri ga al’ummar Najeriya kuwa? Wakilanmu sun tuntubi mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Dokar za ta taimaka – Bello Dallaji

Bello Idris Dallaji: “Dokar hana shan taba a bainar ta yi daidai kuma za ta yi amfani matuka, domin masana sun nuna cewa masu shakar hayakin taba ko sigari sun fi cutuwa a kan wadanda suke zukar tabar ita kanta. Saboda haka idan ka duba za ka ga cewa mutanen da ba su sha sun fi cutawa da hayakin saboda yadda mutane ke shan ta a bayyane kuma a cikin bayin Allah. Musulunci ya kuma nuna mana cewa duk wanda ke shan taba almubazzari ne saboda haka ina goyan bayan dokar hana shan taba a cikin mutane.”