Ko fallasa sunayen masu taurin bashi ya yi daidai?
A farkon watan nan ne aka buga sunayen wasu mutane da kamfanoni masu taurin bashin banki. Ga yadda muhawarar masu karatunmu ta kasance: Fallasa sunayen masu taurin bashi ya yi daidai – Salisu Mai Kananzir Daga Hussaini Isah, Jos Salisu Adamu Mai Kananzir: ‘’Wannan abu da aka yi na fallasa sunayen masu taurin basussukan bankuna […]
A farkon watan nan ne aka buga sunayen wasu mutane da kamfanoni masu taurin bashin banki. Ga yadda muhawarar masu karatunmu ta kasance:
Fallasa sunayen masu taurin bashi ya yi daidai – Salisu Mai Kananzir
Daga Hussaini Isah, Jos
Salisu Adamu Mai Kananzir: ‘’Wannan abu da aka yi na fallasa sunayen masu taurin basussukan bankuna a Najeriya ya yi daidai, domin wannan abu da aka yi, zai taimaka wajen kaucewa durkushewar bankuna da taimakawa wajen dawo da tattalin arzikin kasar nan. Babu shakka masu taurin bashi, sun taimaka wajen karya tattalin arzikin kasar nan.”
An yi daidai – Isah Abdullahi
Daga Hussaini Isah, Jos
Isah Abdullahi: ‘’Wannan abu na fallasa sunayen masu taurin bashi da bankuna suka yi ya yi daidai. Bai kamata ma ace sai a yanzu ne da aka sami canjin gwamnati bankuna za su fallasa sunayen masu taurin bashin da suka ranci kudade daga wajensu ba. Domin mutanen nan sun fi karfin kudaden da suka karba.Don haka wannan mataki da aka dauka daidai ne.”
Mun yi maraba da matakin – Yalwa Abubakar
Daga Hamza Aliyu, a Bauchi
Yalwa Abubakar Dawa: “Tabbas abin da bankunan kasar nan suka yi na fallasa sunayen wasu mutane da kamfanoni masu taurin bashi ya yi daidai domin wata kila basu da niyyar biyan kudaden ne don haka aka buga sunayensu a jaridu. Idan mutum yaji haushi sai ya biya su kudin tunda ba kyauta aka bashi ba.”
Fallasa sunayen bai dace ba – Rabaran Maina
Daga Hamza Aliyu, a Bauchi
Rabaran Joshua Ray Maina: “A fahimtata fallasa sunayen masu taurin bashi da bankuna suka yi kwanakin baya bai da ce ba saboda ai lokacin da aka basu basussukan ba’a buga sunayensu a jaridun kasar nan ba. Bankuna sun fi kowa sanin hanyoyin da za su bi domin karban kudin daga wajen masu taurin bashi. Wata kila wasu daga cikinsu suna son yin takara ne don haka aka ce bari a bata musu suna.”
Ya yi daidai – Abubakar dan Ngamdu
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Malam Abubakar dan Ngamdu: “A ganina dangane da kokarin da ake yi na fallasa sunayen masu taurin bashi da ake yi lalle hakan daidai ne. Idan har aka fallasa sunayen masu taurin bashin aka kuma matsa musu suka biya hakan zai zama ishara ga na baya, don nan gaba za a guji aikata almundahana da kudin al’umma. Don haka wannan yunkuri ya yi daida.”
Babu laifi – Shugaba Bunu
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaba Bunu Aliyu: “A ganina yunkurin da sabuwar gwamnatin kasar nan na fallasa masu taurin bashi da ake yi hakan babu laifi. Masu taurin bashi ai so suke su durkusar da kasar nan, don haka fallasa su tamfar wajibi ne don gudun kada su ci gaba dayin rufda ciki a kan dukiyarmu duk da cewar a yanzu ma sun yi abin da suka yi. Don haka lalle gwamnatin tarayya kar ta yi wasa wajen wannan
kyakkyawan kudiri nata domin kuwa hakan daya daga cikin cika alkawarinda suka dauka ne.”