Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:
Mata gyara suke yi – Shola Ajishegiri
Shola Ajishegiri: “A ganina mata taimakawa suke yi wajen gyara matsalar cin hanci ba habaka t ba, suna kuma gyara sauran al’amura da maza suka dade da lalatawa da zaran sun samu dama ta hanyoyi daban-daban, saboda tausayi da sassauci da kuma rashin keta da aka san su da shi, sabanin takwarorinsu maza.”