Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?1
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:
Mata ba su yin almundahana – Yahaya Musa
Malam Yahaya Musa: “Wannan ba gaskiya ba ne. Mafi yawan matsalar cin hanci na faruwa ne a ma’aikatun gwamnati, inda maza suka yi wa mata fintinkau a wajen yawa. Kuma wadanda ke aikata cin hancin na yi ne saboda handama da kuma buri ba wai saboda mata ba, sai dai don ’ya’yayensu da suke tura wa makarantu masu tsada.”