Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?2
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:
Sukan taimaka wa almundahana amma… – Hajiya Nana
Hajiya Nana Maigwanjo: “Eh, mata na taimakawa wajen aikata almundahana amma idan sun samu malamai masu sa su a hanya, idan ka lura irin rauni da tausayin da mata ke da shi. Amma da cewa ka yi su sun fi kwarewa wajen shagali da jin dadi da kuma nuna kawa, to nan mace ta fi kwarewa amma wajen aikata almundahana ko ta taimaka a aikata to ban yarda cewar mata na yi ba kuma idan ka dubi abin da ya faru da wadannan ministoci mata da ake tuhuma, daya ai mota ce ta saya ta kawa. Ita kuwa waccan daya ministar, ina ganin kamar ta rude ne, domin dai duk maganar da ake yi kamar a kansu ake yi. Allah Ya sauwaka.”