Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?3

Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]

Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?3
Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?3

Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:

Mata ne kan gaba a almundahana – Hajiya Hafsatu
Hajiya Hafsatu ’Yarbawa: “kwarai kuwa mata sun fi almundahana ba taimakawa kawai suke yi ba. Dalilina kuwa da na ce mata ke almundahana ba wai taimakawa suke ba shi ne, idan ka dauki misali da Shugabar Majalisar Wakilai da ta gabata da kuma ministoci mata, wadanda aka sauke da wadanda ke kai yanzu irin rawar da suke takawa wajen bacewar kudade da kuma irin yanayin yadda suke gudanar da ayyukansu kuma ganin cewar wadannan mata fitattu ne a idanun duniya sai ya nuna cewar mata ke almundahana ba wai taimakawa suke yi ba kuma ko maza da suke almundahana ai saboda mata suke yi.”