Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?4

Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]

Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?4
Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?4

Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:

Babu shakka mata na taimakawa wajen almundahana – Zayyana Mamman
Zayyana Mamman Mai Walda Malumfashi: “Ida nana batun almundahana ko hanci da rashawa a kasar nan, mata suna taimakawa sosai, domin kuwa idan ka yi misali tun daga zamantakewar iyali, mata kan raina abin da mijinsu ya kawo. Idan ya kawo kadan,. Za ka ji suna cewa gidan wane ba haka ake ba. Wannan  za ta sanya miji ya shiga wani hali, yana iya kauce hanya domin ya samo kudi da yawa don kada a raina masa. Ka ga a nan wa ya taimaka ya kauce? Matarsa. Haka batun yake idan aka zo wajen biki ko suna ko kuma lokacin hidimar Sallah. Za ka ga mata suna kokarin ingiza mazansu domin su rika yi masu hidimomin da suka fi karfin samun su. Dalili ke nan wasu ke yin ha’inci a wuraren sana’arsu ko wurin aikinsu, domin dai su faranta wa matansu rai.