Ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya?5
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma: […]
Abu ne da yake a fili karara cewa almundahana, kashe-mu-raba, aringizo da sauran duk wani nau’in sama-da-fadi sun yi yawa, sun yi kane-kane a kowane lungunan kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko gaskiya ne mata na taimakawa wajen almundahana a Najeriya? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma:
Mata suna taka rawa ga almundahana
– Khalid Imam
Khalid Imam: “Ko shakka babu, ba yadda za a yi a ce mata ba su taimakawa wajen almundahana, cin hanci da rashawa da ya mamaye wannan kasa tamu. Shi hanci da rashawa ba wani abu ne da yake bambance jinsi ba, bai san mace ba kuma bai san namiji ba. Son zuciya ne ke haifar da shi kuma wannan ana samun shi a maza da mata. Abin da kawai ke rage son zuciya shi ne tsoron Allah da kuma kyakkyawar tarbiyya. Duk da cewa maza su suka fi yawa a harkar gwamnati, amma wannan ba zai hana a ce mata ma suna taka rawa ba a wajen cin hanci darashawa a harkar gwamnati ba. Ba zan mance ba, akwai lokacin da matata ta haihu a asibitin gwamnati, nas din da ta zo za ta gaya mani batun, sai da ta nemi in ba ta wani abu, wai na albishir. Duk da cewa ba wani abu ba ne mai yawa na ba ta ba, amma dai da yake roko na ta yi, ba don kashin kaina na ba ta ba, ai ka ga wannan ma bai dace ba.