Ko gawata ba za ta sake yin PDP ba – Tsohon Mashawarcin Gwamnan Gombe

Mako biyu da ficewar tsohon mashawarcin Gwamnan Jihar Gombe kan harkokin tsaro Alhaji Muhammad Babangida Abdullahi daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da keta katin zama dan PDP, sai ga shi an nemi hallaka shi a Gombe. A ranar Juma’ar da ta gabata ne da karfe 9:50 na dare a rukunin gidajen Unguwar Shongo da […]

Ko gawata ba za ta sake yin PDP ba – Tsohon Mashawarcin Gwamnan Gombe
Ko gawata ba za ta sake yin PDP ba – Tsohon Mashawarcin Gwamnan Gombe

Mako biyu da ficewar tsohon mashawarcin Gwamnan Jihar Gombe kan harkokin tsaro Alhaji Muhammad Babangida Abdullahi daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da keta katin zama dan PDP, sai ga shi an nemi hallaka shi a Gombe.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne da karfe 9:50 na dare a rukunin gidajen Unguwar Shongo da ke hanyar Bauchi wasu matasa uku a cikin wata mota mai launin kore mai lambar Gombe BLG 142 AA suka tare shi a wajen hirarsa suka nemi hallaka shi.
Alhaji Babangida Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa yana zaune sai ya ga matasan sun fito daga mota, daya na zaune a ciki suka kama hannunsa za su sa shi a motar sai ya ki, ya ce duk abin da za su gaya masa su fadi a idon jama’a domin bai san su ba kuma bai yarda da su ba. Ya ce nan take dayansu ya ce masa kai yanzu har ka isa ka yi adawa da Gwamna har ka rika zaginsa? “Sai na ce a’a adawa dai ina yi, amma ba na zagi don na samu tarbiyya daga gidanmu, babu yadda za a yi in zagi shugaba ko na gaba da ni,” inji shi.
Alhaji Babangida, ya ce sai daya daga cikinsu ya doka masa wani katon dutse a fuska da niyyar fasa masa ido, ya yi masa rauni a kumatu suka kama shi da kokawa da niyyar su kashe shi, sai Allah Ya ba shi sa’a ya buge su ya gudu cikin unguwa ya tsira. Ya ce bayan ya tsira ne ya wuce asibiti aka yi masa magani aka ce za a kwantar da shi, amma ya ki domin yana gudun za su biyo shi su kashe shi. Ya ce daga nan ne ya wuce ofishin ‘yan sanda ya bada rahoto, suka yi alkawarin gudanar da bincike don gano mutanen.
Alhaji Babangida ya ce babu wanda yake zargi da neman kashe shi illa gwamnatin PDP da Gwamna dankwambo domin matasan ce masa suka yi me ya sa yake adawa da Gwamna, “Ka ga kuwa tunda suka fadi haka ni Gwamnan nake zargi da turowa a kashe ni saboda na bar PDP na kuma ajiye masa mukaminsa. Da sun ce ni ba komai ba ne kuma ba ni da kowa, ficewata daga PDP ba wani abu ba ne, amma sai suka ga ni kowa ne, ina da kowa, shi ya sa suka nemi kashe ni,” inji Babangida.
Ya ce ba shi ba PDP har abada kuma ko gawarsa ba za ta sake yin kuskuren komawa PDP ba, sai APC daga sama har kasa inda ya ce yanzu ne ma ya samu kwarin guiwar kara tallata ‘yan takararsa na APC. Ya ce jam’iyyarsu ta APC a matakin jiha tana shirin daukar mataki kuma ta sanar da uwar jam’iyyar ta kasa abin da ke faruwa da ‘ya’yanta duk da ‘yan takara sun sanya hannu cewa za a yi siyasa cikin lumana, amma sai ga shi ‘yan PDP sun fara karya yarjejeniyar.
Ya kirayi magoya bayan Jam’iyyar APC cewa kada su ce za su dauki doka a hannunsu wajen rama abin da aka yi, suyi hakuri su bar hukuma ta yi aikinta a kai, “Abin da za ku yi kawai shi ne ranar zabe kowa ya fito da katin zabe ya jefa wa APC sai an kada PDP an karya ta an samu canjin da ake nema,” inji shi.