Ko hadin gwiwa da Indiya zai bunkasa harkokin noma a Jihar Katsina?

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa da ke da yanayi mai kyau ta fuskar al’amuran noma da kiwo. Ba tun yau ba, gwamnatoci daban-daban, tun daga gwamnatin mulkin mallaka, sun yi yunkuri daban-daban a zamunansu, na bunkasa harkokin noma a yankin. Sai dai duk da haka, jihar na da bukatar tsari da kulawa […]

Ko hadin gwiwa da Indiya zai bunkasa harkokin noma a Jihar Katsina?
Ko hadin gwiwa da Indiya zai bunkasa harkokin noma a Jihar Katsina?

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa da ke da yanayi mai kyau ta fuskar al’amuran noma da kiwo. Ba tun yau ba, gwamnatoci daban-daban, tun daga gwamnatin mulkin mallaka, sun yi yunkuri daban-daban a zamunansu, na bunkasa harkokin noma a yankin. Sai dai duk da haka, jihar na da bukatar tsari da kulawa ta musamman ta fukar noma, madamar ana son manoma da makiyaya da sauran masu tu’ammali da su, su ci gajiyar dimbin albarkatun da Allah Ya hore wa yankin.
Kamar yadda Gwamnatin Tarayya, a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta kuduri aniyar mayar da hankali wajen bunkasa noma da kiwo, a matsayin hanyoyin samar da ayyukan yi da bunkasa kasa da abinci da kuma samun kudin shiga, haka ma a Jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari ya nuna kudurinsa na farfadowa da dawo da martabar noma da kiwo a sassa daban-daban na jihar.
Kamar yadda bincike ya nuna, jihar na da albarkar kasa, wacce manoma kan iya noma duk wani tsiro da ya hada da masara, shinkafa, dawa, gero, alkama, ridi, auduga da gyada da sauransu daban-daban. Haka kuma, kayan miya da suka hada da tumatiri, tattasai, albasa, barkono da sauransu, ana noma su sosai a jihar.
A yankin kudancin jihar, musamman kananan hukumomin Sabuwa, dandume, Faskari, Funtuwa, Bakori, kankara, Malumfashi, Matazu da Musawa, masana harkar noma sun ce madamar aka samar da tsari ta fuskar noma, za su iya samar da adadin duk wani hatsi da kasar nan ke bukata, ba ma jihar kadai ba. Haka abin yake ta fuskar noman rani a Arewacin jihar, inda kananan hukumomin Jibiya da Kaita da makwabtansu za su iya samar da kayan marmari, alkama, kayan miya da sauran kininsu.
Aminiya ta tuntubi Alhaji AbdulHadi Ahmad Bawa, Mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, dangane da shirin da gwamnatin jihar ke yi dangane da bunkasa al’amuran noma a jihar. Jami’in ya bayyana cewa, harkar noma na daya daga cikin abubuwan da Gwamna Masari ya ba muhimmanci. Ya ba da misalin wani kwakkwaran mataki da gwamnan ya dauka, inda shi da tawagarsa suka ziyarci kasar Indiya, a ranakun 18 zuwa 20 na Nuwamban bara, dangane da samo hanyoyin kulla alaka da kamfanoin harkar noma; ta yadda manoman jihar za su ci gajiyar bunkasa noma ta hanyar zamani.
Kamar yadda ya ce: “Maigirma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ya kai ziyarar aiki a ofishin jakadancin kasar Indiya da ke Abuja, a inda ya gana da Jakadan kasar Indiyan, ya kuma gabatar masa da halin da Jihar Katsina take ciki musamman ta wajen tabarbarewar ilimi da kuma aikin gona sannan da kuma bangaren matsalar ruwan sha. Ya kuma yi masa nuni ga irin gudummuwa da taimakon da muke bukata daga kasar ta Indiya, kasancewarta jagora a cikin kasashe masu tasowa. A karshen wannan ziyara ce Gwamna ya mika wa Jakadan kundin bayanan da aka tattara a kan halin da jihar take ciki, wanda a take Jakadan ya nuna aniyarsa ta tunkarar wadannan bukatu na Jihar Katsina ka’in-da-na’in domin ganin ta inda kasar Indiya za ta taimaka.”
Ya ci gaba da bayyana cewa: “Sakamakon wannan aniya ta Jakadan ce wani kamfani da ke a kasar ta Indiya mai suna MAHINDRA & MAHINDRA ya aiko wa Gwamnan da goron gayyata, domin ziyara ta gani da ido a kasar ta Indiya, domin shaida irin gudunmuwar da kamfanin ke bayarwa ta bangaren bunkasawa tare da saukaka hanyoyi da dabarun noma na zamani. Kuma wannan kamfanin ne ya dauki nauyin tafiyar.” Inji AbdulHadi.
Ya ce wannan kamfani na Mahindra da aka kafa cikin shekarar 1945, an kafa shi ne domin kera kananan motoci da injina amma yanzu ya wuce tsara, tun da a yanzu bayan kananan motocin da tarakatoci, har manyan motoci na aikin hanya yake kerawa, sannan ga hanyoyi da dabaru na musamman na noman zamani, wadanda suke amfani da su wajen taimaka wa kanana, matsakaita da manyan manoma a kasar tasu.
Ya bayyana cewa, taimakon da kamfanin Mahindra yake wa manoma ya fara ne tun daga wajen awo da tantance yanayi da kyan kasa domin tantancewa da zabo irin shuka da zai dace da wuri, domin samun yabanya mai kyau; har ya zuwa yadda za a sarrafa amfanin gona, ajiya da kuma sayarwa a kasuwanni. Domin cin ma wannan buri, wannan kamfani yana amfani da kwararrun ma’aikata ta bangarori daban-daban, sannan kuma ya kirkiri wani irin shago na musamman wanda duk abin da manomi ke nema to, a nan zai same shi ba sai ya yi ta yawo ba. Wannan kuwa ya kama tun daga iri har zuwa su taki da kuma magungunan feshi na kyautata shuka da kuma na kashe kwari.
A wannan ziyara, inji mashawarcin, an zagaya da Gwamna da ’yan tawagarsa zuwa sassan kamfanin, inda ya gane wa idonsa matakai daban-daban da wannan kamfani ke bi wajen kera tarakatocin noma. Daga bisani kuma aka zagaya da su wurin da ake kerawa tare da hada injinan ba da wutar lantarki, injinan noma da kuma babura na hawa da na daukar kayan gona. An kuma gabatar wa wannan tawaga wani matsakaicin inji, wanda ake iya sarrafa shi ya gabatar da duk wani aiki da tarakata za ta iya yi, sai dai abin burgewa wannan inji, an yi shi kamar salon galmar shanu. Injin yana yin kaftu, haro, shuka, huda, girbi, ban ruwa, ba da hasken wutar lantarki da kuma daukar kaya ta hanyar jan bodi ko kuma tirela.
“Bisa la’akari da yadda dubarun noma na zamani suke saukakawa tare da bunkasa harkar noma, wannan ziyara ba karamin alfanu za ta samar wa manoman Jihar Katsina ba, domin wadannan injuna kanana ne da matsakaita, wanda manoma a daidaikunsu ko ta kungiyoyin gama kai za su iya mallaka cikin sauki, ba kamar tarakata ba. Sannan kuma samun ingantaccen iri da sauran magunguna na feshi da sauransu, na kan gaba wajen tabbatar da samun amfani mai kyau. Haka kuma sabbin dubarun ajiyar amfanin gona za su rage yawan asarar da manoma ke yi wajen ajiyar amfaninsu kafin kaiwa zuwa kasuwa.” Inji shi.
Ta fuskar samar wa manoma kayan aiki na zamani kuma masu saukin sarrafawa, ya ce: “Samun wadannan hanyoyi na zamani zai rage amfani da dabbobi, musamman shanu wajen aikin gona. Wannan na nufin za a samu karin nama mai kyau da fatu (kirgi), domin manoma za su sami damar yin turka ta dabbobi. Wannan na nufin za a sami bunkasar tattalin arziki na al’umma da kuma gwamnati, musamman a yanzu da darajar mai ta fadi kasa warwas.”
Ta wadanne hanyoyi Gwamnatin Jihar Katsina za ta amfana da wannan alaka tsakanin kamfanin Mahindra-Mahindra, wajen bunkasa harkokin noma a jihar? Sai mai ba gwamna Masari shawara ya ce: “Wannan alaka za ta samar da fasaha da kimiyyar aikin gona na zamani ga manoman Jihar Katsina cikin sauki kuma da rahusa. Alakar za ta haifar da bunkasa harkokin noma da kiwo, ta yadda mutane da yawa na jihar za su samu aikin yi da sana’o’i, wanda haka zai bunkasa samun kudin shiga ga jihar. Gwamnati za ta samu damar samo wa manoma iraruwan shuka ingantattu kuma masu albarka, sannan za ta samu damar samar da takin zamani cikin rahusa. Kamar kuma yadda za ta samar da kayan aikin noma na zamani.
“Daga karshe, idan aka samu nasarar tafiyar da wannan alaka da yarjejeniya, tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina, bisa shugabancin Alhaji Aminu Bello Masari da kamfanonin noma na Indiya, babu shakka cikin lokaci harkokin noma da kiwo da sana’a za su bunkasa a jihar, kanana da matsakaitan kamfanoni za su wanzu ta yadda kudin shiga ga gwamnati da al’umma za su samu.” Inji mai ba gwamnan na Katsina shawara.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya