Ko har yanzu sarakuna gargajiya suna da tasirin juya akalar talakawansu?

Sarakunan gargajiya su ne ke tare da al’umma kuma su ne ke fada a ji wajen tabbatar da bin doka da oda. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko har yanzu sarakunan suna da tasirin juya akalar talakawansu? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga ra’ayoyinsu: Tasirinsu ya ragu matuka – Babangida Wunti Hamza […]

Ko har yanzu sarakuna gargajiya suna da tasirin juya akalar talakawansu?
Ko har yanzu sarakuna gargajiya suna da tasirin juya akalar talakawansu?

Sarakunan gargajiya su ne ke tare da al’umma kuma su ne ke fada a ji wajen tabbatar da bin doka da oda. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko har yanzu sarakunan suna da tasirin juya akalar talakawansu? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga ra’ayoyinsu:

Tasirinsu ya ragu matuka – Babangida Wunti

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Babangida Wunti: “Maganar gaskiya gwamnati ce ta rage tasirin sarakunar gargajiya a Najeriya, domin a shekarun baya mutane suna mutunta sarakuna fiye da tunanin mutum amma yanzu abun ya sauya. Abun kunya ne a ce Shugaban karamar Hukumar yana gaba da basarake kuma duk inda wani sarki zai je sai shugaban ya ba shi izinin zuwa. Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka rage musu tasiri. Kuma kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, babu wani tanadi da ya yi wa sarakunan gargajiya. Domin a wajen gwamnati sarakuna ba su da wani aiki sai zama a fada don haka wasu ke musu kallon ba su da wani tasiri a tsarin zamantakewar al’umma.”

Har yanzu suna da tasiri a wajen al’umma – Balali Mula

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Ibrahim Ahmed Balali Mula: “Kamar yadda kowa ya sani ne sarakunan gargajiya suna da muhimmanci a tsarin zamantakewar al’umma. Kuma ina tabbatar maka da cewa har gobe suna da tasiri a tsakanin al’umma. Misali, ko dan siyasa ne ya fito takara sai ya je wajen sarakunan gargajiya domin neman albarka saboda sun san cewa suna da tasiri a rayuwar yau da kullum. Akwai wadanda suke cewa kwadayi ya taimaka sosai wajen rage tasirin sarakuna a Najeriya amma duk da haka za mu ci gaba da mutunta su kuma su ma ya kamata su yi nesa-nesa da gurbatattun ’yan siyasa masu neman mulki ido rufe.”

Sarakunanmu sun rasa kima – Yusuf  Musa

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Malam Yusuf Musa Mant: “A gaskiya sarakuna musamman wadanda muke da su a wannan zamanin sun rasa kimar da talakawansu suka yi ta kallonsu da ita a baya. Dalili kuwa shi ne, akasarin sarakunan da muka bude ido kuma muka sani suna da tsoron Allah, sannan suna kwatanta adalci tsakaininsu da talakawan da ke karkashinsu. Ba su nuna kwadayin abin da suke da shi a hannun da kan kai ga tamkar suna so su kwace wa wadanda ke karkashinsu dukiyoyinsu baki daya. Kodayake ba a taru aka zama daya ba, har yanzu wasu daga cikin wadanda muke da su a wannan zamanin suna da wadatar zuci fiye da yadda ake tsammani.”

A can baya sun fi tasiri – Ja’afaru Abubakar

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Alhaji Ja’afaru Abubakar: “Ba a san sarakunan da muke da su a kasahenmu da kimar da aka san su da ita a can baya ba. Dalilina kuwa shi ne, Allah ne Yake bayar da mulki ga duk wanda Ya ga dama kuma a lokacin da ya ga dama. Ka ga ke nan duk wanda ya samu kansa a wannan matsayin yana kasancewa ne jakadan Allah, musamman idan Musulmi ne a tsakanin talakawansa da zai rika wanzar da zaman lafiya tare da kwatanta adalci ba tare da nuna bambancin addini ko na kabila ba. Sai ga shi wasu daga cikin wadannan mutanen a wasu yankunan da su ake hada kai a tayar da zaune tsaye, wasu kuma suna sayar da sarautun gargajiya, maimakon a bi cancanta, sai a bi wanda ya fi ruwan Naira ba tare da an yi alfahari da wani ko wasu ayyuka kwararan da ya yi wa jama’ar yankinsa ba. Babban abin takaici shi ne wasu daga cikinsu sun tsoma kansu ko sun bari an tsoma su cikin harkar siyasa dumu-dumu.”

Ba su da katabus ga talakawa – Alhaji Ado

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Sarkin Hausawan Akinyele, Alhaji Ado Sulaiman: “Tsarin mulkin Najeriya ya riga ya tunkude sarakuna daga yin wani katabus ga talakawansu. Tsare mutunci shi ne tasirin sarki a yanzu. Shugaban karamar Hukuma shi ne a kan gaba da Sarki saboda haka sarakuna ba za su iya bayar da umarni ko juya akalar talakawansu ba domin an tsame su daga yin hakan. Tsare mutuncinsu shi ne tasirinsu.”

Tasirin sarakuna ya ragu – Tahir Zubairu

Kabir Yayo Ali, a Ibadan

Ustaz Tahir Zubairu: “Abun duniya ne ya rufe wa sarakuna idanu ya kai su ga sayar da mutuncinsu ga son duniya fiye da rungumar talakawa tsakani da Allah. Yin hakan ya rage musu tasiri a idanun jama’a. Saboda haka ba za su iya juya akalar talakawansu ba, domin talakawan sun gane cewa ba domin su ake yi ba, suna yi ne domin kansu.”