Ko Harajin Kan Sarki Na Naira 50 Da Bankuna ke Cirewa Ya dace?

Tun a makonnin da suka gabata ne bankuna a fadin kasar nan suka fara cire Naira 50 daga asusun ajiyar duk wanda ya yi huldar da ta kai ta Naira 1,000 da sunan ‘Harajin Kan Sarki.’ Kamar yadda dokar haka ta tanada, an yi haka ne da nufin farfado da harkokin gidajen waya da kuma […]

Ko Harajin Kan Sarki Na Naira 50 Da Bankuna ke Cirewa Ya dace?
Ko Harajin Kan Sarki Na Naira 50 Da Bankuna ke Cirewa Ya dace?

Tun a makonnin da suka gabata ne bankuna a fadin kasar nan suka fara cire Naira 50 daga asusun ajiyar duk wanda ya yi huldar da ta kai ta Naira 1,000 da sunan ‘Harajin Kan Sarki.’ Kamar yadda dokar haka ta tanada, an yi haka ne da nufin farfado da harkokin gidajen waya da kuma sama wa kasa karin kudin shiga. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko wannan haraji ya dace a wannan lokaci? Ga abin da mutane suka ce:

Harajin Kan Sarki bai dace ba – Muhammadu Sani

Muhammad Sani Jume: ‘’A gaskiya tsakani da Allah, wannan haraji na Naira 50 da ake cire wa masu fitar da kudi a bankuna bai dace ba. Saboda masu karamin karfi wadanda dan abin da suke cirewa a banki bai taka kara ya karya ba, su ne zai shafa.  A ce duk Naira dubu daya da mutum ya fitar a banki sai an cire masa Naira 50, a gaskiya ana takura wa jama’a, musamman idan aka dubi irin abubuwan da suke tafiya a halin yanzu na tabarbarewar harkokin kasuwanci a kasar nan. Don haka, a gaskiya bai kamata a ci gaba da karbar wannan haraji ba. Saboda haka ina kira ga Babban Bankin Najeriya da wannan gwamnati kan a duba wannan al’amari, a dakatar da shi; domin wannan abu zai kare ne kan talakawa.’’

Harajin Kan Sarki ya dace – Manu Isah

Manu Isah Idris: ‘’A gaskiya ya dace a ci gaba da karbar wannan haraji na kan sarki a bankunan kasar nan, domin abu ne mai kyau; musamman idan aka yi la’akari da halin da kasar nan take ciki na rashin kudi, domin a halin yanzu farashin man fetur ya fadi a kasuwar duniya. Don haka gwamnati take neman hanyoyin da za ta sami kudaden shigar da za ta yi wa talakawan kasar nan ayyukan raya kasa. Kuma wannan haraji na Kan Sarki na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta bi ta samu kudaden shiga. Saboda haka ni a wurina, wannan tsari yana da kyau kwarai da gaske.”

Amfanin harajin nan kadan ne – Mu’awiya Abubakar

Mu’awiya A. Abubakar: “Ni a ganina, bullo da wannan shiri na karbar harajin Naira hamsin daga masu ajiya a bankunan kasar nan, ko akwai amfani amma ba yawa, domin idan ba an hada shirin tare da ci gaba da wayar wa jama’a kansu a kan munufar karbar harajin ba sai an samu baraka. Da dama mutane wadanda suka yi wa shirin mummunar fahimta, za su fara jan kafa wajen kai kudadensu su yi ajiya a bankuna ko kuma wasu su fara janye ajiyarsu a hankali daga kowane banki saboda rashin fahimtar abin da shirin ya kunsa. Don haka ya kamata tun da farko duk wani shiri da ake bukatar bullo da shi da nufin amfanin al’ummar kasa, to ya kamata a bi ana ilimantar da jama’a kafin aiwatar da shi, muddin ana yi ne da nufin ya amfani jama’a; to kada a yarda a bar su a cikin duhu. Dalilina na fadin haka kuma shi ne, ina ganin wayewar kanmu da ci gabanmu ta zamani bai kai na irin wadancan manyan kasashen ba da muke gani.

Ina goyon bayan Harajin Kan Sarki – Lawan Inuwa

Lawan Inuwa: “A gaskiya ni a irin tawa fahimtar da na yi wa wannan shiri na Babban Bankin Najeriya, da farko za a duba dalilin bullo da wannan shiri saboda ta haka ne za a iya a yi wa wannan shiri kyakkyawar fahimta, domin idan muka duba a yanzu a cikin yanayin da kasar take ciki da ainihin halin da gwamnati ta tsinci kanta a ciki take kuma fama da shi. Domin a sanin kowa, kasar nan ta dade tana fuskantar matsalar cin hanci da karbar rashawa. Wannan yana daya daga manyan matsaloli da suka taimaka wajen saka kasar nan cikin talauci da fitintinu kafin zuwan wannan gwamnain ta kama aiki. Saboda haka ni ina ganin wannan harajin Naira hamsin bai kai a tsaya ana cece-kuce a kanta ba, muddin za a tara a yi wa al’ummar kasa aikin da zai kawo ci gaba da samun magance matsalolin da gwamnati take ciki; to lallai za a iya cewa ya dace kwarai da gaske.

Ban gamsu da Harajin Kan Sarki ba – Hassan Hamisu

Hassan Hamisu Daram: “Ban gamsu da wannan haraji na kan sarki ba, soboda yin haka zai kara jefa talakka cikin damuwa, karshe ma babu wani alfanu da talakka zai samu daga wadannan kudi da za a rika diba a jikinsa, duk da bayanan da aka yi a kansu. Ga shi ba a yi la’akari da cewar mafi yawan ma’aikata irin wannan asusu na yanzu-yanzu suka bude saboda samun karbar kudinsu cikin sauki. To, mai karbar Naira dubu talatin ko kasa ga haka nawa zai tashi da su? An cire kudin cefanan sati ke nan. Don haka ba ni goyon bayan yin hakan.”

Harajin nan bai dace ba – Sani Abdullahi

Sani Abdullahi Mati: “Bai dace a rika cira Naira hamsin a kan kowace Naira dubun da mutun zai dauka a banki ba. Dalilin farko shi ne, ba a taba yin haka a kasar nan ba, sannan ga mai karamin karfi an kara durkusar da shi. Wani Naira 1000 zai bari daga cikin albashinsa, wanda in an cire Naira 50 ba ita kadai aka cira ba sai dai a ce an cire Naira 100 a takaice saboda ba zai karbi Naira 950 ba saboda ba ma za a ba shi hakan ba a bankin. Saboda haka wannan ba ci gaba ba ne amma cire Naira 40 ta sanarwar banki (alert) ba a ji dadi ba,ina ga wannan?”