Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka: Rabi’u Yunusa […]
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:
Rabi’u Yunusa Kura: “Ba da mukamin sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati gaskiya ni a nawa ra’ayin bai dace ba, domin komai a muhallinsa yake; don haka a bar shi a hakan. Abin da nake nufi shi ne, aikin gwamnati daban haka kuma tafiyar da harkokin mulkin gargajiya daban kuma wani abin ma sau tari ai sarautar gargajiya gado ake yi kuma ana bai wa mutun ne idan ya gada kuma ya zamanto yana fada ana tafiyar da harkokin sarauta da shi, sabanin abin da ake yi yau.
“Idan an samar da dokar da za ta hana wannan an yi daidai, domin sau tari wadanda ake ba wadannan mukamam sai ka taras saye ya yi ko kuma an ba shi ne ba domin ya cancanta ba kuma me ya sa ba a kiran mutumin da ke kan titu, wanda yake taimaka wa jamaa bakin gwargwadon hali, sai minista, gwamna, sanata ko dan majilisar wakilai ko kuma wani babban jami’in gwamnati, wanda idan ya zo fada sau daya sai kuma wata shekara? Amma idan ba ya aikin gwamnati, wannan ba laifi ba ne, don idan an samar da dokar hana wannan ba da sarautar, ni a nawa ra’ayin an yi daidai.”