Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?2
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka: Ban ga […]
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:
Ban ga laifin ba ma’aikata sarautun gargajiya ba – Moyegun Jide
Moyegun Jide: “Ni a nawa ra’ayin, ban ga wata illa ba, domin mutum na aikin gwamnati kuma yana rike da mukamin sarautar gargajiya, sai dai mukamin ya danganci wane irin ne aka ba mutum. Idan dai sarauta irin ta karramawa ce, wadda bai bukatar mutum ya yi aiki kodayaushe, wannan ba wani laifi a cikinta. Misali, idan sarautar ba za ta kawo wa aikinsa cikas ba, wannan ba wani laifi ba ne. “Kuma wasu sarautar gargajiyar na jeka-na-yika ne kurun wasu kuma suna bukatar ka, don haka idan dai irin wannan sarautar ce ba wani laifi. Amma idan sarautar da za ta bukaci mutum ya kasance tare, to bai dace a ba ma’aikacin gwamnati ba.”