Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?3
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka: Hafizu Balarabe […]
An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:
Hafizu Balarabe Gusau: “Tabbas wannan dokar ta dace, a hana duk wani ma’aikacin gwamnati amsar mukamin sarauta, ko wace iri ce kuwa. Domin kuwa wasu suna fakewa da guzuma ne suna harbin karsana. Saboda sau da yawa wasu na amfani da waɗannan mukaman suna yaudarar al’ummarsu, don samun kwarjinin da ba sai sun yi wa jama’a ayyukan da suka ɗaukar wa gwamnati da jama’arsu alkawarin za su yi tsakani da Allah ba. Uwa-uba, masu kagen sarauta don ci da gumin talakawa, don wasu ma saye suke yi, ba cancanta ake kallo ba. An maida abin ne kasuwanci.”